Yau Najeriya za ta kece raini da Masar a Kaduna
A yau Juma’a ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Masar a garin Kaduna a wasan neman zuwa gasar cin kofin Afirka na shekarar 2017. Za a yi wasan ne da misalin karfe biyar na Yamma agogon Najeriya.Tuni Hukumar shirya kwallon kafa ta […]
A yau Juma’a ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Masar a garin Kaduna a wasan neman zuwa gasar cin kofin Afirka na shekarar 2017. Za a yi wasan ne da misalin karfe biyar na Yamma agogon Najeriya.
Tuni Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayyana kudin tikitin shiga wasan. Hukumar ta ware Naira dubu 1 ga masu sha’awar kallon wasan a wurin da manyan baki ke zama (Grand Stand) yayin da ta ware Naira 300 ga duk mai son ya kalli wasan a bangaren ya-ku-bayi (Popular side).
Filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna dai yana cin ’yan kallo ne kimanin dubu 25, kuma an sha gudanar da manyan wasanni irin wannan a cikinsa.
Najeriya dai tana rukunin G ne, rukunin da ya kunshi kasashen Masar da Tanzaniya da kuma Chadi.
Kawo yanzu Masar ce take kan gaba a rukunin da maki 6 daga wasanni biyu sai Najeriya ke biye da ita da maki 4 a wasanni biyu sai Tanzaniya mai maki daya a wasanni biyu yayin da Chadi ta zama ta karshe a rukunin ba tare da ta samu maki ko daya ba daga wasanni biyu.
Kenan idan Najeriya ta samu nasara a wasan na yau, za ta karbi ragamar rukunin G da maki 7 yayin da Masar kuma za ta koma ta biyu da maki 6. Amma idan Masar ta samu nasara za ta hada maki 9 kenan yayin da Najeriya kuma za ta kasance da maki hudu, kuma akwai yiwuwar ta koma ta uku idan Tunisiya ta lallasa Chadi da kwallaye masu yawa.
Sai dai a ranar Talata mai zuwa 29 ga wannan wata da muke ciki ne Najeriya za ta bi Masar gida don yin wasa karo na biyu a filin wasa na Aladendria da ke Masar. Wadannan wasanni biyu ne za su tantance matsayin kowace kasa a gasar.
kasashen da suka kasance na daya da kuma na biyu a kowane rukuni ne za su haye gasar cin kofin Afirka a shekarar 2017 da zai gudana a tsakanin watan Janairu zuwa na Fabrairu a kasar Gabon.
Masana harkar kwallo suna ganin wannan wasa na Najeriya da Masar ne zai tantance karfin kungiyoyin kwallon kafar biyu kuma duk kasar da ta sake aka yi mata sakiyar da ba ruwa, to sai buzunta.
Ana sa ran dubban masoya kwallon kafa ne za su yi tururuwar shiga filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna a yau don kashe kwarkwatar idanu.
Tuni hukumomin tsaro suka sha alwashin samar da cikakken tsaro don ganin an yi wasan lafiya kuma an tashi lafiya ba tare da an samu wata matsala ba.