Yau Najeriya za ta yi sabon ango
Yau ne Najeriya za ta yi sabon ango inda Muhammadu Buhari zai kasance shugabanta bayan cikar wa’adin mulki Shugaba Jonathan da ya sha kaye a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga Maris da ya gabata. Shugabannin kasashe 54 ne ake sa ran za su halarci bikin rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari […]

Yau ne Najeriya za ta yi sabon ango inda Muhammadu Buhari zai kasance shugabanta bayan cikar wa’adin mulki Shugaba Jonathan da ya sha kaye a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga Maris da ya gabata.
Shugabannin kasashe 54 ne ake sa ran za su halarci bikin rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari wanda zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon angon Najeriya a yau da safe a dandalin Eagle Skuare da ke Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi takara sau uku a baya, zai zamo angon ne bayan ya shiga tarihi a matsayin wanda ya yi takara har sau hudu, inda ya yi takara da Obasanjo a 2003 da marigayi Umar ‘Yar’aduwa hudu a 2007 da Jonathan a 2011, amma sai a wannan karon (2015) da ya sake karawa da Jonathan ya samu nasara, sai dai kuma zai shugabanci kasar ne a daidai lokacin da Najeriya take fama da masassara sakamakon yadda wadansu manyan cututtuka guda hudu suke addabarta wadanda suke hana ta sakewa a ’yan shekarun nan. Masassarar wadda za ta iya shafar ’ya’yanta 36 wato jihohi da kuma mowarsu Birnin Tarayya Abuja, sun hada da cin hanci da rashawa da rashin zaman lafiya da rashin aikin yi da kuma karancin makamashi wato wutar lantarki da man fetur da dangoginsa.
Sabon Shugaban kasar da mafi yawan gwamnonin jihohi da galibinsu suka fito daga Jam’iyyar APC wadanda suka samu nasara a zabbubbukan da suka gabata tare da yin waje da ’yan takarar Jam’iyyar PDP da ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar nan, za su hau mulki ne a daidai lokacin da kudin shigar kasar nan ya yi kasa sosai, kuma a lokacin da jama’ar Najeriya ke cike da gurace-guracen samun sa’ida da sauki daga dimbin matsalolin da tattalin arziki da rayuwa suke ciki.
Shugaba Muhammadu Buhari yana da babban aiki a gabansa na cika alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe, inda ya yi alkawarin kawo canji mai ma’ana a kan yadda ake tafiyar da harkokin kasar nan.
Muhammadu Buhari mai shekara 72 a duniya, ya bayyana cewa cin hanci da almundahana ba za su samu wurin zama a gwamnatinsa ba, lamarin da ke haifar da tsoron cewa akwai yiwuwar ya doka gudumarsa a kan ’yan siyasar da suka saba watanda da dukiyar jama’a, kamar yadda ya yi a lokacin mulkinsa na soji. Kuma duk da ya yi alkawari ga Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan cewa kada ‘ya ji tsoron komai’ kuma ba zai yi bi-ta da kulli ba, akwai alamun ba zai iya kawar da kai daga wadansu bangarori da ake ganin an tafka tabargaza ba, musamman bangaren man fetur da ya yi kaurin suna wajen aikata almundahana.
Shi kansa Jonathan ya ji a jikinsa cewa akwai alamun za a binciki gwamnatinsa wanda hakan ne ya sanya a jawabinsa na ban-kwana ga Majalisar Zartarwarsa a shekaranjiya Laraba ya ce, idan ma har Buhari zai yi bincike bai kamata ya takaita binciken kan gwamnatinsa ba, kamata ya yi ya faro binciken tun daga 1960 lokacin da Najeriya ta samu ’yanci. Shugaba Jonathan dai ya yi rawar gani wajen amincewa da shan kaye inda ya zama daya daga cikin shugabannin Afirka da suka mika wuya ba tare da jan kafa ba. Masu sharhi na da yakinin Buhari zai karfafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, inda ya yi alkawarin zai bayyana dukiyar da ya mallaka domin tabbatar da gaskiya da amana.
Za a ci gaba da tuna gwamnatin Jonathan kan yadda ta bari Boko Haram ta yi karfin da ta jawo salwantar rayukan kimanin mutum dubu 15 tare da raba miliyan daya da rabi a fafatawar da aka dauki shekara shida tana yi da soji.
Duk da ana ganin mayakan Boko Haram suna tsaka mai wuya, amma masana tsaro na ganin har yanzu da sauran rina a kaba, idan aka lura da miyagun hare-haren da suke kaiwa da kuma yiwuwar su sake tattaruwa a kan iyakokin kasar nan don ci gaba da miyagun ayyukansu.
Buhari ya rika nanata batun sake fasalin soji tare da kawo karshen almundahana a bangaren soji wanda ya jawo musu rashin ingantattun makaman da za su yi yaki da su. Sai dai akwai bukatar sake inganta aikin sojin ya tafi kafada-da-kafada da shirye-shiryen inganta rayuwa da tattalin arziki ta yadda za a tuttuge tushen abubuwan da suke kawo tashin hankali da suka hada da rashin aikin yi a tsakanin matasa da rashin ayyukan ci gaba a Arewa. Wata barazanar kuma ita ce ta kartar kasar da tsofaffin mayakan Neja-Delta ke yi kan ko a ci gaba da kebe wani kaso na musamman na dukiyar man fetur da ake haka a yankinsu ko su koma ruwa don ci gaba da gwagwarmaya, musamman idan gwamnatin Buhari ta ki kara wa’adin shirin yi musu afuwa da zai kare aiki a kwanan nan.
Sannan ga matsalar ci gaba da bayar da tallafin mai ko janye shi, matsalar da shi kansa Buhari ya ce bai santa ba duk da ya taba yin Ministan Man fetur a baya. Matsalar tallafin mai dai ita ce ta jawo kasar nan ta tsaya cik na fiye da mako daya a tsakiyar wannan wata, sakamakon shiga yajin da masu dakon mai suka yi, har ta kai ana sayar da man fetur lita daya a kan Naira 200 zuwa 400. Tilas ne Buhari ya magance batun tallafin man ta hanyar tayar da matatun mai su kama aiki gadan-gadan.
Masassarar rashin aikin yi a kasa baki daya, kuma akwai bayanan da ke nuna cewa matasa wadanda sune ke da kusan kashi biyu bisa uku na jama’ar Najeriya miliyan 170 na fama da rashin aikin yi, inda ita kanta Jam’iyyar APC ta ce akwai kimanin mutum miliyan 110 da suke fama da talauci.
Don haka sai sabon Shugaban kasa Buhari ya tashi tsaye wajen samar da masana’antu da farfado da wadanda suka kwanta ciki har da farfado da sufurin jiragen kasa da na sama da sauransu kafin ya cimma nasara a wannan fage.
Angon na Najeriya zai fuskanci matsala wajen magance wadannan matsaloli ganin ya zo a lokacin da kasar ke fama da karancin kudin shiga sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.
bangaren makamashi da ya hada da wutar lantarki da man fetur da dangoginsa na daya daga cikin sassan da Buhari zai fuskanci matsala, a Juma’ar makon jiya ne gwamnatin Najeriya ta ce yanzu kasar nan tana iya samar da wutar lantarki mai karfin megawatt dubu daya da 327 ne kacal, wanda shi ne mafi karanci a tarihin kasar nan kuma kasa da na lokacin da Buhari ya yi mulki a 1983 zuwa 1985.
Farfado da wutar lantarki ana ganin zai zama kashin bayan farfado da daukacin harkokin tattalin arzikin kasa, to amma babban kalubalen da Buhari zai fuskanta shi ne yadda jami’an gwamnatocin baya suka mayar da wannan bangare saniyar tatsa tare da sanya siyasa da son zuciya daga bangaren shugabannin gwamnatocin.
Ana sa ran Buhari ya rufe ido sosai wajen sake fasalin wannan bangare tare da duba batun sayar da bangaren rarraba wutar lantarki ta yadda za a samu gasar da za ta haifar da dan mai ido ga kasar nan. An ruwaiti cewa Jam’iyyar APC ta yi alkawarin inganta karfin wutar lantarki zuwa megawatt dubu 12 nan da zuwa karshen wa’adin farko na mulkinta.
A yau dai ‘yan Najeriya sun yi wa Buhari barka da zuwa tare da yi masa fatan alheri, shi kuma Jonathan da ya mika masa mulki suka yi masa fatan ya sauka lafiya.