Yau ne hutun Maulidi – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ba da hutu a yau Juma’a, domin al’ummar Musulmi su samu zarafin gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW). Ministan Al’amuran Cikin Gida Janar (ritaya) Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya, a wata takardar sanarwa ga manema labarai da Babban Sakataren Ma’aikatar cikin gida, Abubakar Magaji […]

Gwamnatin Tarayya ta ba da hutu a yau Juma’a, domin al’ummar Musulmi su samu zarafin gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).
Ministan Al’amuran Cikin Gida Janar (ritaya) Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya, a wata takardar sanarwa ga manema labarai da Babban Sakataren Ma’aikatar cikin gida, Abubakar Magaji ne ya sa hannu a Larabar da ta gabata, a Abuja.
Dambazau ya yi kira ga dukkan Musulmi da sauran ’yan Najeriya da su yi addu’ar samun zaman lafiya, ci gaba da hadin kai a kasa.
Ya kara yin kira ga dukkan ’yan Najeriya da su goyi bayan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kokarin da take yi na gina kasa mai karfi, sannan ya na wa ’yan Najeriya fatan bikin Maulidi cikin farin ciki.
Musulmai na yin bikin Maulidi ne duk shekara a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a matsayin ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Su kuma, kungiyar ’Yan Jarida Musulmi ta Najeriya, suna taya ’yan Najeriya da dukkan Musulman duniya da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Sun fadi haka ne a sakon Maulidi da shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdulrahman Balogun ya bayar, inda ya yi kira ga hakuri da daidaituwa a kowane yanayi.
Ya ce yana cikin Sunnar Annabi Muhammad (saw), zaman lafiya da hakuri da juna da Musulmi, har ma da wadanda ba Musulmi, ba su yi kwaikwayo da wadannan halayen na annabi a matsayin girmamawa a gare shi.
“Muna takaici da damuwa sosai ganin yadda ake komawa kan tafarkin rashin tsari a siyasa da karin musgunawar da ke faruwa a gidaje daban-daban a Najeriya, ganin 2018 ta karato,” inji Balogun.