Yau Shekara 16 da rasuwar Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Shekara 16 da aka yi wa Malam kisan gilla yana jagorancin Sallar Asuba, amma har yanzu an kasa gano wadanda suka yi wannan aika-aika

Yau Shekara 16 da rasuwar Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Yau ake cika shekara 16 da wasu ’yan bindiga suka yi wa shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, kisan gilla a yayin da yake limancin Sallar Asuba.

A safiyar Juma’a, 13 ga Afrilu, 2007, wasu mahara suka kutsa cikin masallacin da ke gidan Sheikh Ja’afar a unguwar Dorayi da ke Kano, suka harbe shi a kirji, a yayin da yake sujjada, wanda hakan ya yi ajalinsa.

Kararuttukan Sheikh Ja’afar, musamman na Tafsirin Al-Kur’ani, sun yadu a sassan duniya, kuma har yanzu yana samun yabo game da zurfin iliminsa da iya bayani a saukake gami da amfani da kyawawan lafazin da kuma iya mu’amala.

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya kasance babban abin koyi musamman ga dalibai da malamai musamman ganin yadda ba ya shakkar tsage gaskiya cikin hikima tare da amfani da hujjoji masu gamsarwa da bayani mai warkarwa da kwararan misalai.

Malam bai bar shugabanni ba, bai bar masu sarautar gargajiya ba, haka kuma bai bar ma’aikatan gwamnati ba, bai bar ’yan kasuwa ba, kamar yadda bai bar talaka ba.

Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, balo- balo zai fito ya fayyace masa illar haka. Ya yi yaki da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baki.

Ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa kuma kararuttukansa na da farin jini har yanzu, shekara 16 bayan ya koma ga Mahaliccinsa.

Tunawa da Sheikh Ja’afar Adam

An fara wallafa a Afrilu, 2020

Malam ya rasu ne a wani lokaci da al’ummar Musulmi take matukar bukatar muhimmin malami irinsa.

Mutum ne shi da ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen karatu da karantarwa, fadaka da fadakarwa, ankara da ankararwa.

A lokacin da mafi yawan malaman addini suka zama makwadaita, shi Malam Ja’afar sai ya zama daban, ya kasance wanda ya san kansa kuma ya rike mutuncin kansa.

A lokacin da wadansu malaman suka siffantu da karkatar da mabiyansu saboda neman girma da neman abin duniya, Malam Ja’afar ya kasance kaifi daya.

Ya dora koyarwarsa bisa turba daya, wato bisa hujja mai inganci ta Alkur’ani da Hadisi da Ijma’in Malaman Sunnah magabata.

Wannan hali ne ya ba shi damar kasancewa jajirtacce, wanda ba ya kyuya ko kasala.

A kullum yana cikin nazari da bincike kuma ba ya furta wata fatawa ba ya ambata kowane karatu, face yana da hujja da kwakkwarar madogara.

Malami ne da ya kauce wa al’amuran kungiyanci.

Idan gaskiya ta zo, ba ya shayin fadinta, ya alla ga ’yan Izala ko ga ’yan Shi’a ko ga ’yan Darika ko kuma ga Kirista da ma wadanda ba su da addini.

A lokacin da ya fara ganin take-taken marigayi shugaban ’yan Boko Haram, Malam Muhammad Yusuf, Sheikh Ja’afar ya yi iyaka kokarinsa wajen fadakar da shi, game da fitinar da yake neman kunnowa ga al’umma.

Amma Muhammad Yusuf ya yi kunnen uwar shegu da hudubar Ja’afar, sai ga shi kuwa abin da ya hango ya tabbata. A yau Kungiyar Boko Haram ta zama annoba ga al’umma.

Marigayi Sheikh Ja’afar ya haifar da sauyi mai girma ga al’umma, musamman ma ga matasa maza da mata, inda suka fahimci tsantsar abin da Musulunci ke koyarwa.

Ta hanyar wa’azozinsa, al’umma sun karu sosai da nagartaccen ilimi kuma ana ci gaba da amfana.

Matasa sun fahimci tsantsar abin da ake nufi da rayuwa, sun gane tasirin neman ilimi, sun gane tasirin neman aiki ko sana’a, kamar yadda suka gane illar zaman kashe wando.

A karantarwarsa, Malam bai bar bai bar wani bangare na al’umma ba.

Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, balo-balo zai fito ya fayyace masa illar haka; Ya yi yaki da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baki.

Ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa.

Wani abin takaici shi ne, har zuwa yau shekara 16 da kisan gillar da aka yi wa Malam, babu wani da aka kama daga cikin wadanda suka gudanar da aika-aikar.

Tarihin Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Malam Ja’afar Mahmud Adam an haife shi ne a ranar 12 ga Fabrairun 1960, a garin Daura ta Jihar Katsina.

Ya samu gurbin karatun gaba da firamare a 1984, inda ya shiga Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnati da ke (GTC) Gwale, wacce a yanzu ake kiranta da Kwalejin Larabci ta Gwamnati (GAC), Gwale.

Ya kammala a 1988, daga nan ya samu gurbin ci gaba da karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina a Saudiyya.

Ya yi karatunsa a can na tsawon shekara hudu, inda ya kammala a 1993.

Marigayi Malam Ja’afar ya kasance: “Ina-ka-fito-nazari, Ina-za-ka-da’awa.”

Gaba dayan rayuwarsa ta kasance a hidimar Musulunci.

Muna rokon Allah Ya jikansa da gafara, Ya amshi shahadarsa, Ya ci gaba raya ayyukansa a fadin duniya.

Allah Ya yi masa sakayyar zaluncin da aka shuka masa, Ya tona asirin makasansa da duk wadanda suka ba da goyon bayan haka ta tabbata.

Allah Ka tada mana da magajinsa, wanda zai ci gaba da haskaka addininKa ga al’umma.

Malam Ja’afar Adam, muna tuna ka, muna yi maka addu’a a kullum. Allah Ya jikanka!

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara