Yau take ranar cika-ciki da cin jela a Kasar Hausa

Yadda al’adar take a Gidan Sarki da Madabo.

Yau take ranar cika-ciki da cin jela a Kasar Hausa

Duk shekara ranar 10 ga watan Muharram na Kalandar Musulunci, ana gudanar da al’adar cika ciki da cin jelar dabbar da aka yi layya da ita a ranar Babbar Sallah a yankunan Hausawa da ke Arewacin Najeriya.

Wannan al’ada duk da ta ja baya sosai, mutane  da dama na sane da ita, sai dai rashin tarihin samuwarta. Ko mene ne asalin samuwar wannan rana?

Nasir Wada Khalil manazarci ne akan Al’adu da Tarihi a Jihar Kano, ya kuma yi wa Aminiya karin haske kan samuwar wannan rana a Kasar Hausa, da kuma sauran al’adun da ake rayawa albarkacin watan da ranar.

“Abinda ke faruwa shi ne duk farkon shekara idan ta zo a 10 ga wata lokacin Ashura ake yinta. Kuma Bahaushe ya kirkire ta kamar al’adu da dama ne domin taimakawa mutane. Shi ya sa ma a cika-cikin ake cewa a bai wa mutane abinci, a shafa kan maraya da sauransu.

“Rana ce mai muhimmanci a watanni shekaru na Bahaushe, domin kamar yadda Bature da Mususlinci ke da wattani 12 a shekara, Bahaushe ma na da na sa: Muharram, Safar, Rabbi-Rabbi, Tagawan Farko, Tagawan Karshe, Gambon Wata, Azumin Tsoffi, Sallar Tsoffi, Azumin Du Gari, Karamar Sallah, Watan Bawan Sallah, Sallah Babba.

“To shi Muharram a cikinsa ake al’adar Cika-Ciki, Cin Jela, da bada Kudin Shara, a Rabbi-Rabbi ake Takutaha, sauran watannin ma duk da al’adar ake rayawa a cikinsa.

“Amma ita al’adar Cika-Ciki, Larabawa ne suka zo da ita dalilin cinikayya da ake yi a tsallaken Sahara ya sa aka samu hakan ga kuma daidaiton addini. Sune lokacin Sallah wato ranar 10 ga wata, suke yanko wa tun daga bayan dabba har a zo jela.

“Sai su ajiye shi har sai 10 ga watan Muharram wata guda cif ke nan, sannan za a cinye. Shi kuma naman jela shi ne wanda ya fi kowanne bangaren dabba ajiyuwa.

Sarrafa Jelar kafin dafawa

Kasancewar ana ajiye jelar na tsawon wata daya ne, akwai bukatar samar da hanyar da za ta ajiyu ba tare da ta lalace ba.

Nasir Wada Khalil ya ce akwai hanyoyi da dama da ake yin haka, da suka hada da busarwa, soyawa, ajiye danyarta, tananawa.

“Kin san yadda Bahaushe ke ajiyar nama a binne shi a Kakide, wasu na yin haka. Wannan shi ne zai hana shi lalacewa tsawon wannan kwanakin. Amma wanda aka fi yi shi ne a rataye ta bushe, ta yadda idan da mai sai dai ya diga kasa, ga iska ko’ina, sai a tsaga ta saboda kar ta rube.

“Wannan ita za a dauko idan 9 ga wata ta yi, sai a wanke ta sai a kara da wani nama mai lafiya, a ci a bai wa mutane.

Sauran al’adun da ake rayawa ranar cika-ciki

Khalil ya ce wasu daga cikin al’adun da ake rayawa a ranar ba su da alaka da addini illa camfi, wasu kuma suna da ita.

“Ana yin hakan ne don yi wa mutane dabara su yi aiki. Misali a ce idan ba ka ci ka koshi ba za a cika maka ciki da wuta, da diban ruwa rijiyoyi 7 a hada a sha, don mutum ya sha ruwan Alkausara, da saka zare a allura sau 7 don a dace da tsallake siradi a ranar lahira. Duk wanna ba su da asali camfi ne.

“Amma al’adar cin abinci da su shafa kan marayu, da sadaka duk masu kyau ne da suke da alaka da addini. Amma ba farilla ba ne, hanya ce kawai ta sada zumunci. Sannan kuma tunda ranar ana azumi, an samu ladan shan ruwan wadanda aka bai wa.

Yadda al’adar take a Gidan Sarki da Madabo

“A gidan Sarki ana yin wainar shinkafar da ake kira mai bakin karfe (ana sarrafa ta yadda za ta shafe sa’a 72 a ajiye ba ta lalace ba a ci da zuma) da Finkaso, da Sinasir, da miya da nama iri-iri, da zuma a raba a gidan malamai, limamai, da yaran gidan Sarki a kuma ci a gidan Sarkin.

“Sarkin Kano marigayi Ado Bayero har dinki yake yi ya raba amma ba kowacce shekara ba, saboda ya gwada wa mutane cewa ba addini ba ne, amma duk abin da mutane za su yi su kyautata zumuncinsu, su jikan na baya da su, ana karfafa musu guiwa.

A Madabo kuma, duk ranar 10 bayan na yi duk wadancan da muka fada a baya, bayan sallar Isha, idan ka je gidan Limamin Madabo ana sanya wa mutane kwalli kala biyar, uku a dama biyu kuma a hagu saboda tsari.

“Yadda ake sanyawa ma na da tsari; za a fara ne da biyu daga dama biyu a hagu sai daya kuma a dama. Hikimar hakan sun ce shi ne haka Ma’aikin Allah (S.A.W) yake saka kwalli.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira