Yau wa’adin da Hukumar FIFA ta dibar wa Najeriya zai cika
A karo na uku kenan Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) take diba wa Najeriya wa’adi don ganin ta sasanta dambawar shugabanci a Hukumar NFF ko kuma ta dage kasar daga shiga harkokin wasanni har illa masha Allahu. A wannan karo ma hukumar ta sake dibarwa kasar zuwa yau Juma’a 31 ga watan […]
A karo na uku kenan Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) take diba wa Najeriya wa’adi don ganin ta sasanta dambawar shugabanci a Hukumar NFF ko kuma ta dage kasar daga shiga harkokin wasanni har illa masha Allahu. A wannan karo ma hukumar ta sake dibarwa kasar zuwa yau Juma’a 31 ga watan Oktoba ko dai ta sasanta dambarwar shugabancin Hukumar NFF ko kuma ta dage ta daga shiga harkokin wasannin da take shiryawa a kowane mataki.
Kamar yadda kwafen wasikar da hukumar ta aikawa Hukumar NFF a ranar Talatar da ta gabata ta nuna, FIFA ta ba Najeriya zuwa yau Juma’a, 31 ga watan Oktoba ta nemi mafita a hukuncin da wata kotu a Jos ta yanke na dakatar da sabon shugaban Hukumar NFF da aka zaba kwanankin baya a garin Fatakwal Mista Pinnick inda kotun ta ce Mista Chris Giwa ne ya kamata ya zama zababben shugaba ba Pinnick ba.
Shi dai Chris Giwa, an zabe shi ne a zaben da wani bangare na Hukumar NFF ya yi a Abuja a kwanakin baya, zaben da bai samu amincewar Hukumar FIFA da wasu bangare na NFF ba. Akan haka ne aka sake shirya sabon zabe a garin Fatakwal inda aka zabi Mista Pinnick da ya samu amincewar Hukumar FIFA da ta NFF.
Bayan an kammala zaben ne sai Mista Chris Giwa ya daukaka kara a wata kotun daukaka kara da ke garin Jos, inda kotun ta dakatar da Pinnick a matsayin shugaba kuma ta maye gurbinsa da Mista Chris Giwa a karshen makon jiya, al’amarin da ya kawo rarrabuwar kawuna a Hukumar.
Da Hukumar FIFA ta samu labarin hukuncin da kotun ta zartar ne ita kuma ta aiko da wasika ga Hukumar NFF cewa ta dibar mata wa’adin zuwa yau Juma’a, ko dai a mayar da Mista Pinnick a matsayin shugaban hukumar ko kuma ta dakatar da Najeriya daga shiga dukkan harkokin wasanni da hukumar ke shiryawa har illa masha Allahu.
Idan Hukumar FIFA ta dage Najeriya, kenan kasar ba za ta halarci gasar cin kofin Afirka da zai gudana a badi a kasar Maroko ba. Haka kuma akwai yiwuwar ita ma kungiyar kwallon kafa ta mata watau Falcons ba za ta halarci gasar cin kofin kwallon kafa na mata na duniya da zai gudana a badi a kasar Kanada ba.
Idan za a tuna, sau biyu hukumar take dage Najeriya daga shiga harkokin wasanni a wannan shekara saboda zargin da hukumar take wa gwamnati na tsoma baki da gwamnatin tarayya take yi a harkokin wasanni na kasar. A watan Satumba da na Oktoban wannan shekara ce dai Hukumar ta aika sakonnin gargadi ga Najeriya a kan yiwuwar dageta daga shiga harkokin wasanni muddin gwamnati ta ci gaba da yin katsalanda.