Yau za a binne gawar marigayi Cif Solomon Lar

A yau Juma’a ne za a binne gawar marigayi tsohon Gwamnan Jihar Filato kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa na farko Cif Solomon Dau-shep Lar a mahaifarsa garin Langtang a Jihar Filato. Cif Solomon Lar ya rasu ne a ranar 9 ga Oktoban bana a kasar Amurka.Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne […]

Yau za a binne gawar marigayi Cif Solomon Lar

A yau Juma’a ne za a binne gawar marigayi tsohon Gwamnan Jihar Filato kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa na farko Cif Solomon Dau-shep Lar a mahaifarsa garin Langtang a Jihar Filato. Cif Solomon Lar ya rasu ne a ranar 9 ga Oktoban bana a kasar Amurka.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya karbi gawar marigayin a filin jirgin saman Abuja, bayan da aka kawo gawar daga daga Amurka.
A ranar Litinin da ta gabata an an je yi gawar marigayi a dakin taro na Lady Kwali da ke otel din Sheraton a Abuja, inda ’yan uwa da abokai suka gabatar da jawabai kan rayuwar marigayin.
Sai kuma a ranar Talata aka kai gawar marigayin zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke Abuja don girmamawa ga marigayin.
Daga nan aka dauki gawar zuwa garin Lafiya fadar gwamnatin Jihar Nasarawa don al’ummar jihar su yi wa gawar marigayin gani na karshe, a matsayinsa na wanda ya mulki jihar a lokacin da take cikin tsohuwar Jihar Filato. Daga nan ne aka wuce da gawar marigayin zuwa garin Langtang inda a shekaranjiya Laraba’ya’ya da ’yan uwan marigayin suka gabatar da addu’o’i na musamman a cocin COCIN da ke garin Langtang.
Daga nan aka dauko gawar marigayin zuwa garin Jos inda aka kai ta harabar Babbar Kotun Jihar da Gidan Gwamnatin Jihar da kuma hedkwatar cocin COCIN.
A yau Juma’a kuma ana sa ran za a kawo gawar marigayin babban filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos inda ake sa ran dubban mutane daga ko’ina za su yi adu’o’i ga marigayin. Daga nan sai a dauki gawar zuwa garin Langtang don binnewa.
Da yake zantawa da ’yan jarida kan irin karramawar da gwam-natin Filato ta yi wa marigayin, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Abraham Yiljap ya ce tuni gwamnatin jihar ta sauya sunan Jami’ar Jihar zuwa sunan jami’ar Solomon Daushep Lar.