Yau Za a binne Ooni na Ife
A yau Juma’a za a binne marigayi Ooni na Ife Oba Okunade Sijuwade. dan marigayin Yarima Adetokunbo Sijuwade, ya bayyana rasuwar marigayin a shekaranjiya Laraba, inda ya bayyana cewa za a binne shi a yau Juma’a. dan marigayi Oba Sijuwade ya bayyana wa manema labarai aGidan Gwamnati da ke Osogbo cewa a jiya ne gawar […]

A yau Juma’a za a binne marigayi Ooni na Ife Oba Okunade Sijuwade. dan marigayin Yarima Adetokunbo Sijuwade, ya bayyana rasuwar marigayin a shekaranjiya Laraba, inda ya bayyana cewa za a binne shi a yau Juma’a.
dan marigayi Oba Sijuwade ya bayyana wa manema labarai aGidan Gwamnati da ke Osogbo cewa a jiya ne gawar marigayin za ta iso Najeriya daga Landan kuma a binne ta da karfe 10:00 na safiyar yau.
Shi ma da yake magana a wurin taron manema labaran, Gwamnan Jihar Osun Alhaji Rauf Aregbesola ya ce “marigayi Ooni yana wakiltar kasar Yarbawa ne kuma ya yi iyakar kokarinsa wajen daukaka martabar masarautun gargajiyar da ke jihar.”
Gwamna Aregbesola, wanda ya karanta sakon tes na karshe da ya samu daga Ooni a wajen taron manema labaran ya ce marigayi sarkin ya shaida masa rashin lafiyarsa, inda ya kara da cewa zai tafi Landan domin neman magani.
A cikin sakon marigayin ya ce: “Mai girma, har yanzu ba ni jin dadi, don haka zan tafi kasar waje a duba lafiyata, don haka na mika gwamnatinka a karkashin kular Ubangiji.”
A ranar Juma’a ce Gwamnan ya bayyana cewa ya samu sakon tes daga basaraken kafin ya bar kasar nan kuma zai sanar da jama’a abin da sakon ya kunsa a lokacin da ya dace.
Ya bayyana rasuwar Ooni na Ife da babban rashi ga jihar da al’ummar Yarbawa, inda ya ce sarki ba ya mutuwa a kasar Yarbawa, domin “Sarki ba ya mutuwa,” saboda mutane ba su cewa sarki yam utu a kasar Yarbawa.
Oba Solomon Omisakin, Obalufe na Iromo kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Ife da Babban Basarake Cif Joseph Ijaodola, Lowa na Ile-Ife, duk sun tabbatar da abin da dan marigayi Sijuwade ya ce.
Sun mika godiya ga al’ummar Jihar Osun kuma sun roki Ubangijin Ya ba su wani sarki da zai shahara kamar yadda marigayi Ooni ya yi.
Taron ganawa da manema labaran ya samu hakartar ’yar Ooni Misis Aderounmu Fadeyi, da wakilan Majalisar Masarautar Ife.
Sai dai a daidai lokacin da ake tsakiyar batun binne marigayi Ooni na Ife ne sai kuma aka shiga yada jita-jitar cewa wanda za a binne su tare da Ooni na Ife wanda ake kira Abobaku ya gudu jim kadan da samun labarin rasuwar sarkin, lamarin da bisa ga al’adar Yarbawa in haka ya tabbata za a dakatar da bukukuwan binne marigayin.
An ce a bisa al’adar Yarbawa, sarki ba ya mutuwa shi kadai. Kuma ana binne shi tare da wasu mutane. Kuma a nan ne Abobaku yake shigowa.
An ce Abobaku yana rayuwa ne tare da sarki kuma a binne su tare. A bisa al’ada akwai zuriyar da za ta rika sarauta yayin da za a samu zuriyar da suke sadaukar da kansu ga al’adar da aka yi imani da ita ta mutuwa tare da sarki.
Abobaku kan ji dadin rayuwa cikin daula lokacin rayuwar sarkinsa.