Yau za a fara duban watan azumin Ramadan
Idan an gani kuma hukumomin da suka dace suka tabbatar, Sarkin Musulmi zai sanar kuma gobe Talata a tashi da azumi a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan.
A yau Talata al’ummar Musulmi a Najeriya da Saudiyya da sauran ƙasashen duniya za su fara duban jinjirin watan Ramadan, kafin faɗuwar rana.
Tun da farko Fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ta buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duban watan a yau Talata, 29 ga watan Sha’awa.
Idan an gani kuma hukumomin da suka dace suka tabbatar, Sarkin Musulmi zai sanar kuma gobe Talata a tashi da azumi a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan.
Idan ba a gani ba, za a cika watan Sha’aban kwana 30, sa’annan a tashi da azumi ranar Alhamis.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Masu Larurar Ulcer Za Su Gudanar Da Azumin Ramadan Ba Tare Da Matsala Ba
- An ƙona masallaci kan rikicin ƙabilanci a Fatakwal
Tuni dai al’ummomin Musulmi suka fara shirye-shiryen azumin watan Ramadan mai alfarma, wanda ake yawaita ibada a cikinsa da neman samun Rahama tsawon kwanaki 29 ko 30.
Yin azumin watan Ramadan na daga cikin rukunan Musulunci biyar, kuma ya kunshi barin ci da sha da saduwar aure da yasassun kalamai da dangoginsu daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.
Yin azumin Ramadan wajibi ne ga kowane Musulmi baligi, lafiyayye mazaunin gida.
An yi rangwamen yin sa ga matafiyi da mata lafiya da mata masu jinin al’ada ko jinin biƙi da tsofaffi masu rauni, amma za su yi ramako bayan watan azumin.
Waɗanda ba za su iya ramako ba kuma za su ciyar da mutum mutum ɗaya a madadin kowane azumi ɗaya.
Amma ƙananan yara da mahaukaci da wanda ba Musulmi ba, azumi bai wajaba a kansu ba.
Ana so Musulmi su yawaita ibada a Ramadan, musamman karatun Alkur’ani da zikiri da sadaka da taimakon mabuƙata da sallar dare—musamman domin dacewa da daren Lailatul Ƙadari a darare 10 na ƙarshen watan.
Kazalika ana buƙatar yin Itikafi musamman a kwanaki 10 na ƙarshen watan, da kuma neman dacewa da da sauran falalolin wannan watan mai alfarma.