Yau za a fara Gasar Al-Kur’ani ta Duniya a Saudiyya
Mahaddata 166 daga kasashen 117 za su shafe kwana 11 suna fafatawa a Masallacin Harami da ke birnin Makkah
Yau Juma’a za a bude Gasar Al-Kur’ani ta Duniya karo na 43 a kasar Saudiyya, inda gwarazan gasar za su samu kyautar Riyal miliyan hudu, kimanin Naira miliyan 800.
Gasar Al-Kur’ani ta Duniya ta Sarki Abdulaziz wadda ta kunshi tsantsar hadda da kuma tafsiri, za ta gudana ne a Masallacin Harami da ke birnin Makkah inda mahaddata 166 daga kasashen 117 za su shafe kwana 11 suna fafatawa.
- Tinubu ya sake tura malaman addinin Musulunci Nijar
- Najeriya ce kasa ta 11 a yawan masu amfani da intanet a duniya
Ministan Harkokin Musulunci na Saudiyya Abdelatif Al Alsheikh, ya sanar cewa a karshen gasar, wadda ma’aikatarsa ta shirya, wanda ya zo na daya zai samu kyautar Riyar 500,000, kimanin Naira miliyan 100.
Al Alsheikh, ya ce a watan Maris na shekarar nan ma’aikatar ta gudanar da gasar haddar da tafsirin Al-Kur’ani na cikin kasar inda gwarazan suka samu kyautar Riyal miliyan 3.3, kimanin Naira 660.
Ya ce mahaddata 3,000 ne suka shiga ganar, inda daga cikinsu maza 58 da mata 47 suka kai matakin karshe, a karshe aka zabi mutum 18 daga kowane jinsi a matsayin gwarazan shekara na kasar.