Yau za a fara gasar La-Liga ta Sifen
A yau Juma’a 21 ga watan nan ne ake sa ran za a fara gasar rukuni-rukuni na kasar Sifen da aka fi sani da La-Liga. Kimanin makwanni biyu kenan da aka fara irin wannan gasa a wadansu sassa a kasashen Turai. A Ingila, an shiga mako na uku kenan da fara gasar firimiya inda ake […]
A yau Juma’a 21 ga watan nan ne ake sa ran za a fara gasar rukuni-rukuni na kasar Sifen da aka fi sani da La-Liga. Kimanin makwanni biyu kenan da aka fara irin wannan gasa a wadansu sassa a kasashen Turai. A Ingila, an shiga mako na uku kenan da fara gasar firimiya inda ake sa ran za a yi wasanni zagaye na uku a wannan mako.
A wasan da zai gudana a yau shi ne na kulob din Malaga da na Sebilla. Wasan zai gudana ne da misalin karfe bakwai da rabi na dare agogon Najeriya. A jibi ne kuma za a yi wasannin da ake ganin sun fi zafi watau a tsakanin mai rike da kofin FC Barcelona da kuma Athletic Bilbao. Barcelona ce za ta bi Bilbao gida a wasan. Za a yi wasan ne da misalin karfe biyar da rabi agogon Najeriya. Sai wasa a tsakanin kulob din Sporting de Gijon da Real Madrid da misalin karfe bakwai da rabi na dare agogon Najeriya.