Yau za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya

Maniyyata kimanin 65,000 daga Najeriya za su sauke farali a aikin Hajjin 2024

Yau za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya

Maniyatta aikin hajji

A Laraba za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali a aikin Hajjin bana.

Jirgin sahun farkon zai tashi ne a Kebbi da maniyyatan jihar, kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar.

Kimanin maniyyata 65,000 ne ake sa ran za su sauke farali daga Najeriya a aikin Hajjin bana.

Hukumar ta ce ana sa ran tashin jiragen maniyyata biyu a kullum daga filayen jiragen sama 15 da aka ware a fadin Najeriya, har sai an kammala kai su Kasa Mai Tsarki.

NAHCON ta bayyana cewa tana sa ran kammala kwashe maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya kafin ko a ranar 10nga watan Yuni, 2024.

Aminiya ta ruwaito shugaban NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, yana cewa maniyyatan za su shafe akalla kwanaki hudu a birnin Madina domin yin ziyara kafin su wuce Makkah domin yin Umrah da aikin Hajji.

A ranar Laraba 14 ko Alhamis 15 ga watan Yuni ake sa ran fara aikin Hajjin 2024, inda za a yi Hawan Arafa a washegari.

Alhazai za su yi Hadaya da jifan farko hadi da Babbar Sallah a washegari.