Yau za a fara raba katin zabe a Sakkwato … Limamai za su fadakar a Jigawa
Yau Juma’a ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) za ta fara raba katin zabe na dindindin ga mutanen Jihar Sakkwato inda ake sa ran za a kamala zuwa jibi Lahadi.kungiyar Zaman Lafiya da ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah a Jihar Sakkwato sun gabatar da taron fadakar da jama’a muhimmancin karbar rajistar musamman a […]
Yau Juma’a ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) za ta fara raba katin zabe na dindindin ga mutanen Jihar Sakkwato inda ake sa ran za a kamala zuwa jibi Lahadi.
kungiyar Zaman Lafiya da ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah a Jihar Sakkwato sun gabatar da taron fadakar da jama’a muhimmancin karbar rajistar musamman a yankunan karkara.
A taron Kungiyar Zaman lafiya da aka gudanar a Makaratar Haddar kur’ani ta Sarkin Musulmi Maccido ranar Asabar Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko sun yi kira ga jama’ar jihar su fito kwansu da kwarkwata su karbi katin don ba su damar zaben shugabannin da suke so.
Malaman addini irin su Malam Ibrahim Liman da Abubakar Mabera da batagarawa da Malam Jabir Sani Maihula sun gabatar da nasihohi ga jama’a kan wajibcin karbar katin zaben.
A bangaren Izala wadda ta shirya taronta a masallacin Buhari dan Shehu, Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Abubakar Usman Mabera ya ce duk wanda ya kai shekara 18 ya je ya karbi katin, “domin sai da katin ne muke iya zabar shugabannin da za su wakilce mu, kuma duk yadda kake son ka canja shugaba in ba wannan katin to ba za ka iya ba,” inji shi.
Ya bukaci shugabannin kungiyar a kananan hukumomi su shiga kowane lungu da sakon jihar domin fadakar da mutane kada su yi sake da damarsu, kada wani ya ce gona zai tafi.
Hukumar Zabe ta kasa a Jihar Jigawa ta ce za ta yi amfani da limamai da fada-fadan coci wajen fadakar da al’umma muhimmancin yankar katin zabe.
Da yake jawabi a wajen taron da hukumar ta shirya wa ’yan siyasa da kungiyoyin sanya ido kan zabe Alhaji Ibrahim Bagobiri ya ce hukumar ta yi shiri mai kyau domin aikin rajistar, kuma ya bukaci jama’ar jihar su fito domin amsar katin rijistar zaben da za a yi gaba domin su samu damar kada kuri’arsu a lokacin zaben 2015.