Yau za a kece-raini tsakanin Mbappe da gwaninsa Ronaldo
Kylian Mbappe ya ji rauni a fuska, wanda hakan ya sa yake amfani da kariyar fuska
A yau Juma’a ce za a fafata wasan kwata-fainal a Gasar Nahiyar Turai ta bana da ake bugawa a ƙasar Jamus.
Wasannin yau guda biyu masu zafi ne, inda za a fafata tsakanin Faransa da Portugal, sannan a fafata a tsakanin Jamus mai masaukin baƙi da Spain.
- Uba ya ɗaure ɗansa tsawon kwanaki uku babu abinci a Bauchi
- Jerin jiragen alfarma 10 da Najeriya ta dakatar
Ƙasar Faransa ta doke Beljiyum da ci ɗaya mai ban haushi, inda Faransa ta zura ƙwallo ɗaya tilo awasan a minti na 85, bayan da ɗan wasan gabanta Kolo Muani ya yi ƙoƙarin jefa ƙwallo amma ɗan wasan bayan Beljiyum, Jan Vertonghen ya ci gidansu.
A ɓangaren Portugal ta sha da ƙyar ne, inda ta samu nasarar yin waje da ƙasar Slovenia da ci 3-0 a bugun finareti a wasan da aka fafata a ranar Litinin.
A wasan, wanda aka yi tunanin Portugal za ta lallasa Slovenia, wankin hula ya kai su dare, inda sai da aka buga minti 90, sannan aka buga ƙarin minti 30 amma babu ci, kafin aka kai ga bugun finareti, inda Golan Portugal Diego Costa ya ceci ƙasarsa.
Ƙasar Portugal ta samu finareti bayan an ƙara lokaci, inda Ronaldo, wanda har yanzu bai zura ƙwallo ko ɗaya ba a gasar ya ɓarar, wanda hakan ya sa fitaccen ɗan wasan ya fashe da kuka.
Golan Portugal, Diego Costa ne ya buge finareti uku na ’yan wasan Slovenia: Josip Ilicic da Jure Balkovec da kuma ta Benjamin Verbic Yanzu hankali ya koma ne kan fitaccen matashin ɗan wasa, Kylian Mbappe, inda zai fafata da gwaninsa, Cristiano Ronaldo.
Idan ba a manta ba, Kylian Mbappe ya ji rauni a fuska, wanda hakan ya sa yake amfani da kariyar fuska, lamarin da ya ce ba daɗi.
Mbappe ya sha bayyana cewa shi ne magajin Ronaldo, inda ko bayan amincewa zai koma Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya fito ya bayyana farin cikinsa da haka.