Yau za a rada sunan jaririn da Safiya Musa ta haifa
Idan ba za ku manta ba dai a shekarar da ta gabata muka kawo muku labarin fitacciyar jaruma Safiya Musa ta yi auren sirri a ranar 15 ga watan Fabrairun 2013, inda aka daura mata auren da Alhaji Abdullahi Yakubu dankumbo a garin Garkida da ke Jihar Adamawa.A yanzu dai jarumar ta haifi namiji, kuma […]

Idan ba za ku manta ba dai a shekarar da ta gabata muka kawo muku labarin fitacciyar jaruma Safiya Musa ta yi auren sirri a ranar 15 ga watan Fabrairun 2013, inda aka daura mata auren da Alhaji Abdullahi Yakubu dankumbo a garin Garkida da ke Jihar Adamawa.
A yanzu dai jarumar ta haifi namiji, kuma yana cikin koshin lafiya kamar yadda wata majiya da ke kusa da jarumar ta bayyana wa Aminiya.
Majiyar ta ce Safiya ta haihu ranar 10 ga wannan watan amma kasancewar ba ta jin dadi sai aka daga ranar suna zuwa ranar Juma’a mai zuwa (yau ke nan).
“Ta haihu lafiya ba tare da wata tangarda ba, sai dai daga baya ta daina jin dadin jikinta, amma a yanzu ta samu lafiya har an sanya ranar Juma’a mai zuwa a matsayin ranar suna.” Inji majiyar.
Majiyar ta ce ma’auratan suna cikin farin ciki.