Yau za a samu sakamakon zaben Zambiya

A yau Juma’a ne ake sa ran samun sakamakon zaben kasar Zambiya bayan kammala kada kuri’a a shekaranjiya Laraba. An bude rumfunan zabe a kasar ne ranar Talata, amma sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tilasta wa hukumar zaben kasar tsawaita wa’adin kada kuri’ar zuwa ranar Laraba. Domin bai wa wadanda ruwa […]

Yau za a samu sakamakon zaben Zambiya
Yau za a samu sakamakon zaben Zambiya

A yau Juma’a ne ake sa ran samun sakamakon zaben kasar Zambiya bayan kammala kada kuri’a a shekaranjiya Laraba.

An bude rumfunan zabe a kasar ne ranar Talata, amma sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tilasta wa hukumar zaben kasar tsawaita wa’adin kada kuri’ar zuwa ranar Laraba. Domin bai wa wadanda ruwa ya tsare su a gida, fita domin kada kuri’arsu.
Bukatar gudanar da zaben shugaban kasa ya bijiro ne bayan da wanda ke rike da kujerar wato Shugaba Michael Sata, ya rasu a bara. Wannan ya sama duk wanda ya lashe zaben zai karasa wa’adin mulkin marigayin ne kawai.
Masana dai na ganin takarar tafi zafi ne tsakanin Mista Edgar Lungu na jam’iyyar Patrotic Front da kuma Hakainde Hichilema na jam’iyyar United Party for National Debelpoment. Kuma wakiliyar BBC a babban birnin kasar Lusaka, ta ce duka ’yan takarar sun yi alkawarin inganta fannin ilimin kasar da kuma samar da ayyukan yi. Rahotanni sun bayyana duk da ruwan saman da ya barke a ranar farko ta zaben, jama’a sun fito sosai domin kada kuri’unsu. Har ila yau, za a kara gudanar da sabon zabe ne a badi, shekarar da wa’adin tsohon shugaban zai kare.