Yau za a yi jadawalin wasan Semi-Fainal a gasar zakarun kulob-kulob na Turai
A yau Juma’a 24 ga watan Afrilun 2015 ne ake sa ran Hukumar shirya wasan kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) za ta gudanar da jadawalin wasan kusa da na karshe (Semi-Fainal) a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League. Kulob hudu ne daga kasashe daban-daban suka […]
A yau Juma’a 24 ga watan Afrilun 2015 ne ake sa ran Hukumar shirya wasan kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) za ta gudanar da jadawalin wasan kusa da na karshe (Semi-Fainal) a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
Kulob hudu ne daga kasashe daban-daban suka kai wannan mataki. Kulob din su ne FC Barcelona da na Real Madrid daga Sifen da Jubentus daga Italiya da kuma Bayern Munich.
Za a gudanar da jadawalin ne a Hedkwatar hukumar da ke Nyon a kasar Suwazilan.
Ana sa ran kafofin watsa labarai da gidajen talabijin a sassan duniya za su nuna bikin jadawalin kai tsaye da misalin karsfe 12 na rana agogon Najeriya.
Hukumar ta ce idan aka kammala jadawalin, wasannin farko za su gudana ne a ranakun 5 da kuma 6 ga watan gobe, watau na Mayu yayin da ake sa ran gudanar da wasanni zagaye na biyu a ranakun 12 da kuma 13 ga watan goben.
Sannan akwai yiwuwar kowace kungiyar kwallon kafa ta hadu da takwararta a jadawalin, ma’ana ba a kebe wani kulob don kada ya hadu da wani a jadawalin ba.
Alal misali kulob din FC Barcelona zai iya haduwa da na Real Madrid ko na Jubentus ko kuma na Bayern a jadawalin.