Yau za a yi jana’izar Alhaji Umaru Shinkafi

Yau ake sa ran yi jana’izar fitaccen dan siyasar nan kuma daya daga cikin masu fada-a-ji da ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi, Marafan Sakkwato wanda Allah Ya yi wa rasuwa a shekaranjiya Laraba a wani asibitin birnin Landan da ke kasar Ingila.’Yarsa Hajiya Fatima Umaru Shinkafi wadda ita ce Kwamishinar […]

Yau za a yi jana’izar Alhaji Umaru Shinkafi
Yau za a yi jana’izar Alhaji Umaru Shinkafi

Yau ake sa ran yi jana’izar fitaccen dan siyasar nan kuma daya daga cikin masu fada-a-ji da ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi, Marafan Sakkwato wanda Allah Ya yi wa rasuwa a shekaranjiya Laraba a wani asibitin birnin Landan da ke kasar Ingila.
’Yarsa Hajiya Fatima Umaru Shinkafi wadda ita ce Kwamishinar Kasuwanci da Masana’antu ta Jihar Zamfara wadda ta tabbatar wa Aminiya da rasuwar mahaifin nasu, ta ce ya hadu da ciwon zuciya ce na wani lokaci.
Ana sa ran isowar gawarsa Najeriya a yau kuma a yi masa jana’iza a makabartar Abubakar na Uku da ke Sakkwato, Hajiya Fatima Shinkafi ta ce ana sa ran yi masa jana’iza yau ko kuma gobe Asabar. Sai dai Kwamishinan Labarai da Al’adu da Yawon Shakatawa na Jihar Zamfara Alhaji Umar Jibo Bukkuyum ya ce yau ake sa ran yi masa jana’iza a Sakkwato
Marigayi Alhaji Umaru Shinkafi mai shekara 79 wanda ya taba rike mukamin Kwamishinan Harkokin Cikin Gida (Minista) tsohon dan sanda ne kuma kwararren masanin tsaro da ya shugabanci tsohuwar Hukumar Tsaro ta kasa (NSO) wadda yanzu aka karkasa kashi uku ciki har da Hukumar SSS.
Bayan ya yi ritaya daga aiki ne daga Hukumar NSO a 1983, a 1985 aka nada shi Marafan Sakkwato kuma a waccan shekarar ce ya auri autar marigayi Sardaunan Sakkwato Hajiya Lubabtu.
Marigayi Alhaji Umaru Shinkafi ya tsunduma harkokin siyasa a Jamhuriyya ta Uku da ta gaza a zamanin Shugaban Soji Janar Ibrahim Babangida inda ya zamo daya daga cikin manyan ’yan takarar da suka fi karfi a rusasshiyar Jam’iyyar NRC a 1992. Sai dai zaben fid da gwani na jam’iyyar bai kamala ba bayan da Shinkafi da Malam Adamu Ciroma suka yi kankankan a zagayen farko kuma kafin a je zagaye na biyu, sai gwamnatin Babangida ta rushe zaben fid da gwanin tare da haramat wa ’yan takarar biyu da wadansu mutum 11 taka rawa a harkokin siyasa.
Alhaji Umaru Shinkafi bai taka rawar siyasa a zamanin Abacha ba, amma a wannan jamhuriyya ya zamo a sahun gaba a tsohuwar Jam’iyyar APP wadda daga baya ta koma ANPP. Hadin gwiwar APP da tsohuwar Jam’iyyar AD ne ya jawo aka hada tikitin takarar Olu Falae da Umaru Shinkafi don takarar Shugaban kasa a zaben 1999, inda tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Mataimakinsa Atiku Abubakar suka kayar da su.   
Marigayi Umar Shinkafi ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya biyar kuma daga cikin ’ya’yansa akwai Hajiya Zainab Atiku Bagudu matar Gwamnan Jihar Kebbi da Hajiya Hadiza Yari matar Gwamnan Jihar Zamfara, kuma shi yayan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi.
Tuni Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnati da jama’ar jihohin Sakkwato da Zamfara kan rashin wannan babban da nasu.
Wata sanarwa da Kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ya fitar ya bayyana marigayin da masanin siyasa kuma kwararre da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen tsara harkokin tsaon kasar nan da ba za a manta da shi ba.
Ya bukaci iyalai da ’yan uwa da abokan marigayin su dauki hakuri wannan rashi kuma su dora kan kyawawan ayyukan da ya yi kuma ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa.
Shi ma a sakonsa na ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihohin Sakkwato da Zamfara Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya bayyana rasuwar dattijo Umaru Shinkafi da babban rashi ga kasa.
Yakubu Dogara wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da Kakakinsa Turaki Hassan ya fitar ya ce Shinkafi wata gad ace ta hade kan kasa da ya yi rayuwa abar koyi.
Shi ma sakonsa na ta’aziyya tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana marigayi Umaru Shinkafi a matsayin mutum mai matukar mutunci da tsentseni kuma dan siyasa mai da’a da Najeriya ta yi asararsa.
Wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Atiku ya bayyana Marafan na Sakkwato da daya daga cikin ’yan siyasa mafiya hazaka da ilimi da gogewa da kuma tsayuwa kan gaskiya da ya taba haduwa da su.
Sauran wadanda suka aike da sakon ta’aziyyarsu sun hada da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru Bafarawa, wadanda suka bayyana rasuwarsa da babban rashi ga Najeriya.