Yau za a yi jana’izar Sarkin Gombe

A yau Juma’a ce ake sa ran za a yi jana’izar marigayi Sarkin Gombe Alhaji Shehu Usman Abubakar, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Talata.Marigayin ya rasu yana da shekara 76, kuma ya yi fama da jinya ta dogon lokaci kafin ya rasu a wani asibitin birnin Landan da ke Ingila.An haifi marigayi […]

Yau za a yi jana’izar Sarkin Gombe
Yau za a yi jana’izar Sarkin Gombe

A yau Juma’a ce ake sa ran za a yi jana’izar marigayi Sarkin Gombe Alhaji Shehu Usman Abubakar, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Talata.
Marigayin ya rasu yana da shekara 76, kuma ya yi fama da jinya ta dogon lokaci kafin ya rasu a wani asibitin birnin Landan da ke Ingila.
An haifi marigayi Sarkin Gombe Usman Shehu Abubakar a ranar 3 ga Maris, 1938 a
garin Gombe fadar Jihar Gombe. Marigayi Sarkin ya yi karatun allo a gida kafin ya shiga makarantar Elementare ta Gombe a 1945 zuwa 1949.
Sarkin ya halarci makarantu daban-daban cikinsu har da Makarantar Midil ta Bauchi daga 1950 zuwa 1952, sai Kwalejin Barewa da ke Zariya daga 1953 zuwa 1958, a 1961 ya tafi Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna (Kaduna Polytechnic).
Marigayi Sarkin Gombe, ya yi babbar diploma a bangaren  kudi, kuma ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi babbar diploma kan gudanar da mulkin kananan hukumomi, sai kuma Jami’ar Ile Ife (yanzu Jami’ar Obafemi Awolowo) inda ya yi babbar diploma a kan zamantakewar al’umma.
Marigayi Sarkin ya fara aiki da Hukumar En’e ta Gombe a tsakanin 1960 zuwa 1962.
A 1967 ya zama babban jami’i inda ya yi aikace-aikace da dama a garuruwan Lafiaji da Pategi a tsohuwar Jihar Kwara, sannan a 1968 ya zama babban jami’inharkokin mulki a Dam din Kainji da ke Jihar Neja, daga bisani aka sake dawo da shi yankin Jalingo da ke yankin Arewa maso Gabas.
Alhaji Shehu Abubakar, ya zama Mataimakin Babban Sakataren a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Arewa maso Gabas. Bayan kirkiro tsohuwar Jihar Bauchi a 1976 sai ya zama Babban Sakatare a ofishin Sauraren Koke-Koken Jama’a, daga nan ya zama Babban Sakataren Ma’aikatar kananan Hukumomi da Gandun Daji a tsakanin 1976 zuwa 1978.
Bayan rasuwar Sarkin Gombe Malam Abubakar Umar a ranar 13 ga Janairun 1984 ne marigayi Alhaji Usman Abubakar ya gaji mahaifinsa a matsayin Sarki na 10, kuma wakili a Majalisar Sarakuna ta Jihar Bauchi. Da aka kirkiro Jihar Gombe a ranar 1 ga Oktoban 1996 sai marigayin ya zama Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Gombe.
Tuni dai Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da gwamnoni da sauran shugabanni suka fara aikewa da sakon ta’aziyyar rasuwar Sarkin ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Gombe, inda suka bayyana rasuwar tasa da babbar rashi da ta haifar da babban gibi mai wuyar cikewa.