Yau za a yi jana’izar tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi
Yau ne ake sa ran yin jana’izar tsohon Mataimakin Gwamna Jihar Bauchi, Alhaji Garba Muhammad Gadi wanda Allah Ya yi masa rasuwa a ranar Talatar da ta gabata a wani asibiti da ke kasar Indiya. Alhaji Garba Gadi wanda shi ne danburam din Karagum a Jihar Bauchi, ya rasu ne yana da shekara 70 a […]

Yau ne ake sa ran yin jana’izar tsohon Mataimakin Gwamna Jihar Bauchi, Alhaji Garba Muhammad Gadi wanda Allah Ya yi masa rasuwa a ranar Talatar da ta gabata a wani asibiti da ke kasar Indiya. Alhaji Garba Gadi wanda shi ne danburam din Karagum a Jihar Bauchi, ya rasu ne yana da shekara 70 a duniya.
Wani aminin marigayin Kyaftin Bala Jibrin wanda ya tabbatar da rasuwar marigayin a yammacin Talata ga wakilinmu ta wayar tarho ya ce ana sa ran isowar gawarsa daga Indiya tare da yi masa jana’iza a yau Juma’a.
Alhai Garba Gadi wanda ya kasance Mataimakin Gwamna Isa Yuguda a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011, Majalisar Jihar Bauchi ta tsige shi daga mukaminsa, amma kotu ta soke tsigewar daga baya. Ya kasance jigo a Jam’iyyar CPC, inda ya jagoranci kwamitin hade jam’iyyun da suka hade suka kafa Jam’iyyar APC mai mulki.
Marigayin wanda ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 15, kafin rasuwarsa shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe.
Marigayin ya halarci makarantar firamare ta santaral da ke Azare kafin ya wuce Babbar Firamaren Kwana da ke Azare a shekarun 1950. Sannan ya halarci Kwalejin Gwamnati da ke Bauchi daga 1962 zuwa 1967.
Sai Kwalejin Barewa daga 1971 zuwa 1973, kafin ya zarce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga 1971 zuwa 1973, inda ya kasance cikin ayarin farko na masu yi wa kasa hidima a Najeriya.
Ya fara aiki da tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas a matsayin jami’in kasuwanci a Ma’aikatar Kasuwanci a 1974 zuwa 1976. Da aka kirkiro Jihar Bauchi a 1976, sai ya koma can da aiki har ya kai matsayin Babban Sakatare. Ya zama Manajan Daraktan Bankin Kasuwanci da Masana’antu (NBCI), daga baya ya zama Manajan Daraktan Kamfanin Fulawa na Zaki da ke Azare a Jihar Bauchi, wanda ya jagorancin kafa shi lokacin da yake bankin NBCI.
A sakonsa na ta’aziyya Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya bayyana rasuwar Alhaji Garba Gadi a matsayin babban rashi ga kasar nan.
A wata sanarwa da Kakakinsa Turaki Hassan ya fitar a Abuja, Dogara ya ce marigayi Garba Gadi, cikakken dattijo ne mai kishin kasa, wanda ya yi rayuwa abar koyi wajen yi wa kasa da al’ummarta hidima. “Mun rasa kwararre kuma gogaggen ma’aikaci, dan siyasar da ke tare da jama’a kuma cikakken dan Jihar Bauchi. Muna mika ta’aziyya ga iyalansa da abokai da kuma al’ummar Jihar Bauchi baki daya,” inji Dogara.