Yaushe Arewa za ta zauna lafiya?
Tun bayan samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka muke fama da rikice-rikicen addini da kabilanci da na siyasa a Arewancin Najeriya.Rikicin Maitatsine shi ne rikicin addini na farko mafi muni da Arewancin Najeriya ta fuskanta a Jamhuriya ta biyu lokacin mulkin marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Tun daga wancan lokacin da aka yi […]
Tun bayan samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka muke fama da rikice-rikicen addini da kabilanci da na siyasa a Arewancin Najeriya.Rikicin Maitatsine shi ne rikicin addini na farko mafi muni da Arewancin Najeriya ta fuskanta a Jamhuriya ta biyu lokacin mulkin marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Tun daga wancan lokacin da aka yi rikicin Maitatsine, an yi ta samun rikice-rikicen addini da na kabilanci daban-daban, kamar daga Arewa zuwa Kudu zuwa Gabas. A farkon 1980 ne aka yi rikicin Maitatsine a Jihar Kano, wanda daga bisani ya bazu zuwa Maiduguri a Jihar Borno da Yola a tsohuwar Jihar Gongola da Gombe a tsohuwar Jihar Bauchi, inda aka yi asarar rayukan dubban mutane Musulmi da Kirista. Bayan wadannan, rikice-rikicen da suka fi muni sun hada da rikicin Zangon Kataf a Jihar Kaduna a 1992 tsakanin Hausawa da Katafawa, wanda daga bisani ya rikide ya koma na addini. A wannan rikici an yi asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa. Sai kuma rikicin Shagamu a Jihar Ogun a watan Yulin 1999 tsakaninYarbawa da Hausawa, bayan kisan wata mata Bahaushiya da wata kungiya mai suna (Oro) ta yi, inda suka ce ta keta ka’idarsu. Kashe-kashen da aka yi wa Hausawa a Shagamu ya sa a Kano ma matasa sun dauki fansa kan Yarbawan da ke zaune a can. Sai kuma a watan Nuwamban 1999, inda wani rikicin kabilanci ya sake barkewa a Unguwar Ajegunle a Jihar Legas tsakanin Kungiyar OPC da ta matasan kabilar Ijaw.
Bayan kwantar da wannan rikici a watan Disamban wancan shekara, an sake samun barkewar rikicin kabilancin a kasuwar Mile 12, tsakanin Kungiyar OPC da Hausawa, bisa dalilan shugabancin kungiyar masu sayar da doya a kasuwar, wato Shukura Yam Sellers Association, wadda kusan Hausawa ne ke rike da shugabancinta, inda aka yi asarar rayuka sama da 200 tare da kone kasuwar kurmus!
Bullo da tsarin shari’ar Musulunci a wasu jihohin Arewa ne ya yi sanadiyar rikicin addini a Jihar Kaduna a watan Fabrairun shekarar 2000, inda nan ma aka yi rikici tsakanin Musulmi da mabiya addinin Kirista wadanda suka nuna rashin amincewarsu da amfani da shari’ar Musulunci a jihar. Rikicin wanda ya bazu zuwa garuruwan Kachiya da Zariya da sauransu, shi ma ya haddasa asarar daruruwan rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa. Bayan wannan rikicin na Kaduna an samu makamancinsa a jihohin Sakkwato da Borno musamman a garin Damboa a Jihar Borno.
An fara samun rikici a Jos tun daga shekarar 2001, wanda asalinsa na siyasa ne a tsakanin ’yan asalin Jihar Filato da Hausa/Fulani da ke zaune a can, kafin daga bisani ya rikide ya koma na addini da kabilanci, kuma ya kasance daya daga cikin manyan rikice-rikicen da aka samu a Najeriya. Rikincin Jos na faruwa ne tsakanin Hausa/Fulani Musulmi da kuma kabilun Filato wadanda akasarinsu mabiya addinin Kirista ne. Bangarorin biyu sun yi takaddama ce kan shugabanci. Kan haka ne wadansu ke ganin baya ga kabilanci da addini, rikicin na Jos na da alaka da siyasa. An samu asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa tun daga lokacin da aka fara zaman-doya-da-manja a garin, wato daga shekarar 2001 zuwa 2010. Rikice-rikicen da aka yi ta yi a Jos a shekarun baya kan bazu zuwa jihohin da ke makwabtaka da ita kamar Gombe da Bauchi.
Ana cikin wannan yanayi ne kuma muka tsinci kanmu a halin da muke ciki a yau, wato rikicin Boko Haram, wanda ya auku a watan Yulin shekarar 2009, inda wadansu matasa karkashin jagorancin Muhammad Yusuf da ke adawar haramta ilimin boko da aikin gwamnati suka kaddamar da yaki kan jami’an tsaro da ofisoshinsu a cikin birninmu na Maiduguri a Jihar Barno. Irin kashe-kashe da zubar da jini da kuma tashe-tashen hankulan da tun farko ake ganinsu a yankin Arewa maso Gabas inda ake fama da talauci, sun bazu zuwa sassan Najeriya da wajenta.
Kungiyar Boko Haram tana iya fitowa fili ta kalubalanci gwamnatin Najeriya a yunkurinta na shimfida abin da a cewarta shi ne tsarin shari’ar Musulunci. Abu ya yi abu, Boko Haram na kai hari ko’ina, duk dai a kokarin cimma manufofinta. Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane, wadanda kuma akasarinsu ’yan Arewa ne, tun daga lokacin da aka fara rikicin a shekarar 2009.
Kungiyar Boko Haram ta fara kai hare-haren farko kan ofisoshin ’yan sanda da na sauran jami’an tsaro. Hare-haren nakiya (bam) na mota na farko ya wakana ne a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja da kuma ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja. Kungiyar ta fadada wuraren da take kai wa hare-hare daga ofisoshin ’yan sanda zalla, zuwa ga masallatai da majami’u har ma da malaman da ba su yarda da akidarta ba.
Tun bayan shekarar 2010, wannan zubar da jini ya bazu ya tsallake iyakar Borno da ma Najeriya. Zubar da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi ya samu karin tallafi ko tagomashi, daga abubuwan da suka faru a kasar Mali daga shekarar 2011 zuwa 2012 inda ’yan tawaye masu alaka da Alka’ida suka kusan kwace kasar, kafin sojojin Faransa su ja musu birki a watan Janairun 2013.
Yau kimanin shekara 10 ke nan muna fama da tashe-tashen hankula da zubar da jini a dalilin kungiyar Boko Haram. Sai ga Jihar Zamfara ma ta dauka, kullum kashe-kashe da zubar da jinin al’umma ake yi. Yau garkuwa da mutune ta zama ruwan dare a Arewa, kai ka ce babu gwamnati a kasar nan. Abubuwan da suke faruwa a ’yan kwanakin nan tsakanin mabiyan (Zakzaky) na Shi’a da gwamnati na sake barazana ga zaman lafiyar kasar, musamman Arewa.
A hakikanin gaskiya wannan kam gwamnatin Najeriya ce ke da alhakin ta-da-zaune-tsaye, musamman idan muka dubi umarnin da kotu ta bayar na a saki shugaban mabiya Shi’ar. Abin da mafi yawancinmu ba su sani ba wadansu kuma suka mance, shi ne, Mohammed Yusuf (Shugaban Kungiyar Boko Haram) wdanasu ’yan tsirarin matasa ya mallaka a birnin Maiduguri, inda suka kaddamar da yaki kan jami’an tsaro da ofisoshinsu a cikin birnin, daga nan kuma kashe-kashe da zubar da jini da tashe-tashen hankula suka zamo ruwan dare a Arewa. A yayin da wadannan tashe-tashen hankula ke bazuwa zuwa wasu sassan Najeriya, har da makwabtanta, fargaba tana kara yawaita saboda gwamnatin Najeriya ta kasa tabuka komai.
Yau kimanin shekara 10 ke nan gwamnatin Najeriya ta kasa murkushe kungiyar Boko Haram, to yaya kuma kungiyar Shi’a, wadda a kusan dukkan kananan hukumomin kasar akwai su? Idan almajiran Mohammed Yusuf da ba su wuce a kidaya su ba an share shekara 10 gwamnatin Najeriya ta kasa murkushe su, to yaya kuma almajiran Zakzaky? Inna lilahi wa’inna ilahi raji’un. Wai shin yaushe Arewa za ta zauna lafiya ne? Wadanne irin zunubai ’yan Arewa suka aikata har Ubangiji Ya jarrabe su da rashin zaman lafiya haka? Zan so ’yan uwana su amsa mini wadannan tambayoyi domin mu san ta hanyar da za mu bi wajen ceto Arewa daga wannan halin da ta tsinci kanta.
A karshe ina rokon Ubangiji Allah Ya sa Arewa ta zauna lafiya, kana kuma Ya hada kawunan dukkan mabiya darikokin addinin Musulunci na kasar nan, amin.
Daga dan uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260