Yaushe jihohin Musulmi suka fara shiga gasar zabar sarauniyar kyau?
Babu shakka abin da ya faru a Jihar Bayelsa a kwanankin baya na zabar sarauniyar kyau babban abin kunya ne ba ga kasar Najeriya kawai ba har da sauran jihohin da ke ikirarin yin shari’a a jihohinsu. Abin bakin ciki da tashin hankali shi ne lokacin da wadansu daga cikin ’yan matan da suka shiga […]
Babu shakka abin da ya faru a Jihar Bayelsa a kwanankin baya na zabar sarauniyar kyau babban abin kunya ne ba ga kasar Najeriya kawai ba har da sauran jihohin da ke ikirarin yin shari’a a jihohinsu. Abin bakin ciki da tashin hankali shi ne lokacin da wadansu daga cikin ’yan matan da suka shiga gasar suka yi ikirarin cewa suna wakiltar jihohin Arewa ne misali an gabatar da Belessing Obi a matsayin wacce take wakiltar Jihar Kano. Ban da ita akwai wacce ta wakilci jihar Zamfara, jihar da aka fara kaddamar da shari’ar Musulunci, akwai wacce ta wakilci jihar Sakkwato da Katsina da sauran jihohin Arewa.
Irin badalar da aka gudanar da a wurin taron da irin tsaraicin da ’yan matan suka nuna ya nuna cewa wadansu daga cikin shugabanninmu na Arewa da suke ikirarin kare shari’ar Musulunci sun yi hannun- riga da ita. Kuma babban dalilin da zai tabbatar maka da cewa da hannunsu a ciki shi ne da har yanzu babu jihar da ta fito ta nisanta kanta daga lamarin. Kuma babu jihar da shugabanninta suka fito suka yi Alla-wadai da bikin, kuma babu jihar da ta karyata cewa tana da hannun ko kuma ta bayar da tallafi ga bikin.
Wannnan ya nuna karara cewa wasu daga cikin shugabanninmu suna yin wasa da hankalinmu. Wannan ya zama kalubale ga malaman addinin su rika gayawa shugabanni gaskiya. Hatta kungiyoyin Izala da darikar Tijjaniya da ta kadiriyya da ta Shi’a da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da ke ikirarin kare musulunci babu wacce ta fito ta soki taron ko kuma ta soki gwamnonin da suka yarda aka tura ’yan matan da suka wakilci jihohinsu.
Wata majiya ta bayyana cewa kowace jiha sai da ta bayar da wasu makuden kudi a matsayin kudin shiga gasar. Kuma an ce wasu gwamnoni sun tura wadanda suka wakilce su a wurin. Alla-wadaran-naka-ya-lalace. Yanzu har gwamnoninmu suna da damar da za su dauki kudadenmu su kashe a harkar da za a saba wa Allah? Kuma jama’a suna gani sun kyale su. Ina masu ba gwamnoni shawara kan harkokin addini? ina majalisun dokokin jihohi? Ina sarakunan gargajiya masu kiran kansu sarakunan Musulunci? Ina sarkin Musulmi? Ku sani Allah zai titsiye ku ya tambaye ku ranar gobe kiyama.
Allah ya saka wa kungiyoyi da matasan da suka taba fitowa suka yi zanga-zanga nuna kin jinin irin wannan bahallatsa a shekarun baya a jihar Kano da Kaduna. Ka da a yi mini mummunar fahimta, ba kira nake yi a fito a yi tashin hankali ba, a’a. Abin da nake nufi shi ne ya kamata shugabaninmu su san abin da ya kamata. Su sani cewa addini shi ne kan gaba ga mutumin Arewa, sannan al’adu kyawawa da ba su saba wa Musulunci ba.
Mu a matsayinmu na ’yan Arewa sauran kabilun kasar nan na girmama mu saboda yadda muke bin addinin musulunci sau da kafa da kuma yadda muke taka-tsantsan ga munanan dabi’u da gaskiya da rikon amana. Ya kamata shugabannin mu su san cewa ’yan kudu na ba za su rika ganin kimar mu ba idan muna biye musu wajen goyawa akidun munana baya. Ai ko turawan Ingila da ake cewa sun fi girmama dan Arewa, ai ba komai ya janyo haka ba sai saboda riko da muka yi da addininmu da al’adunmu kyawawa. Su kuwa ’yan kudu tuni suka yi watsi da na su don samun abin duniya daga wurin Turawa kuma hakan bai tsinana musu komai ba sai rashin girma da kaskanci daga wurin Turawa. Saboda haka ya kamata mu shiga taitaiyin mu, mu san abinda muke yi kada mu bari wasu su rude mu mu manta da asalinmu da kuma inda muka fito da tarihinmu baki daya.
Abu-Mujahid, ya rubuto daga Legas. 08027406827