Yaushe Najeriya za ta farfado daga suman da ta yi?

Shin me ya sa ake jin cewa kila an tsine wa Najeriya?

Yaushe Najeriya za ta farfado daga suman da ta yi?

Najeriya

Kusan shekara 10 ke nan da na yi irin wannan sharhi, na kuma nemi samun amsa daga al’ummar Najeriya, amma kamar jiya-iyau, ba alamun samun sauki ko ficewa daga tarkon tsinuwa da Najeriyar ta fada ciki a tsawon lokaci.

Wannan ne ya sa na ga ya dace mu sake waiwayar wannan batu mu ga ko za mu tsinkayi wani abu da zai zama mafita ga ’yan yau da kuma masu zuwa gobe.

Shin me ya sa ake jin cewa kila an tsine wa Najeriya ne ko kuma ko su wa suka yi wannan tsinuwa, me kuma ya sa?

Kafin mu tsunduma cikin batun da kyau, ya dace mu fahimci yaya batun tsinuwa yake a rayuwar al’umma, musamman a kasa irin tamu?

Lokacin da muke yara kanana, a kauye, ba abin da muka fi jin haushi irin tsinuwa, ko cikin wasa ba a son a ce wani (abokan wasa, tsofaffi da makamantan su) sun tsine maka ko sun nemi a tsine maka ko kuwa iyaye su kama zancen tsinuwa a bakinsu dangane da abin da suka haifa.

Tsinuwa kowace iri ce, bala’i ce, shi ya sa ko tsakanin tsararraki a filin wasa ko kwallo, idan ka yi laifi aka ce ka yi, ka musa, to karyar nan na iya jawo maka tsinuwa, amma ko a lokacin ba a jefa tsinuwar kai-tsaye, sai an yi wasa da ita.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne a ji yara na cewa, ‘Allah tsinini, Allah tsine, Allah tsine uwar mai karya;’ wani kafin ma a ida za ka ji yana cewa don Allah a bari, ku ba ku san wasa ba ne.

Ba fa shi za a tsinewa ba, ‘uwar mai karya’ aka ce, amma kowa ya san tsinuwar da ta bi uwa, na iya bin har ’ya’yanta, saboda haka kada a fara. Ke nan tun a wancan lokaci tsinuwa ko a tsine wa mutum, babbar magana ce.

Tsinuwa bala’i ce. Tsine wa yaro ko daga bakin yaro dan uwansa abin ki ne, domin kuwa ba yaran ne ke yin tsinuwar ba, Allah ne ke tsinewa, duk kuma wanda Allah Ya tsine mawa, ya shiga uku, ya balbalce.

Idan kuwa tsinuwar daga bakin iyaye ta fito, ita ma ba ta da dadi, domin kuwa tofin Allah-tsine na iyaye ya fi komai zafi a cikin al’ummar wancan zamani.

Dukkan wadannan lamurra na tsinuwa suna zuwa bisa tawassuli da Allah, amma tsinuwar iyaye ta fi komai saurin karbuwa saboda kusancin da da iyayensa.

Wannan ne ya sa a wancan lokaci, duk ’ya’yan da iyaye suka tsine mawa za a ga ba sa albarka, ba sa gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata.

Idan har sun rayu, to za a same su ko dai sun zama gawurtattun ’yan iska, su ne yawo kwararo-kwararo ba sana’ar hannu, balle su tabuka komai a rayuwa.

Su ne a gidajen karuwai ko zauna-gari-banza, ba su da aikin fari, balle na baki.

’Ya’yan da iyaye suka tsine mawa ko rigar kwarai ba a ganinsu da ita, kullum cikin tsumma ko ragga, idan tsinuwar ta kai karo kuwa, to sai hauka.

Shi ya sa duk lokacin da muka ga mahaukaci na ta gararamba a titi, ga shi da iyaye da ’yan uwa, ba wanda ya damu da shi, ba abin da ke zuwa a rayuwarmu, sai kila, wannan yaro ko yarinya, ya saba wa iyayensa ne, shi ya sa suka tsine masa, ga shi ya haukace.

Domin a tunaninmu na wancan lokaci, hauka ita ce karshen tsinuwar iyaye ga ’ya’yansu.

Kila zuwa yanzu mai karatu ya fara tambayar kansa, me ya hada batun tsinuwa da Najeriya?

Sai na ga kila tambayar ba ta da wuyar amsawa idan muka dubi halin da kasarmu Najeriya take ciki a halin yanzu, ko kuma daga ’yan shekarun da ba su kasa 15 da suka wuce ba.

Idan na tsaya tsaf sai in ga kamar Najeriya ta yi wa iyayenta laifi ne, irin wanda ’ya’ya ke yi wa iyaye har aka yi mata tofin Allah tsine, ta lalace, ta balbalce, ta shiga duniya tana yawon hauka.

Me ya sa na ce haka? Mu kididdige yadda rayuwar Najeriya take ciki a halin yanzu mu ga idan ba alamun tsinuwa a tare da Najeriya.

A da ko in ce cikin shekara 50 da suka wuce, Najeriya kasa ce mai arziki da wadata, kowa na ji da ita a fagen tattalin arziki, komai game da rayuwar al’ummarta ta fuskar inganta tattalin arziki na gudana yadda ya kamata.

Amma me ya faru cikin wannan tsawon shekaru, arzikin Najeriya ya watse, kasar ta talauce, duk wani ci gaba nata ya durkushe, ta yadda yanzu ba a yi mata komai sai dariya, saboda arzikin da take takama da shi yanzu babu.

Talauci ya cika kasa ta yadda ciyar da kanta da ’ya’yanta ya zame mata matsala. Mene ne wannan in ba alamun tsinuwa ba?

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara