Yaushe ne zaben kananan hukumomin Bauchi?

Aminiya Ku ba ni dama in yi  Allah wadai da kin gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Bauchi. A gaskiya abin takaici ne kin gudanar  mana da zaben kananan hukumomi a Jihar Bauchi, bayan da wasu jihohi irin su Nasarawa da Kano da Yobe yanzu haka suka yi zaben su, haka ake shirin gudanar […]

Yaushe ne zaben kananan hukumomin Bauchi?
Yaushe ne zaben kananan hukumomin Bauchi?

Aminiya Ku ba ni dama in yi  Allah wadai da kin gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar Bauchi. A gaskiya abin takaici ne kin gudanar  mana da zaben kananan hukumomi a Jihar Bauchi, bayan da wasu jihohi irin su Nasarawa da Kano da Yobe yanzu haka suka yi zaben su, haka ake shirin gudanar da zaben a Jihar Katsina. Talakawan Jihar Bauchi suna da bukatar a yi musu zabe.
Kasancewar yau kusan sama da shekaru uku ke nan Gwamna Yuguda, ya ki zaben kananan hukumomin a Jihar Bauchi, ya sake kakaba wa talakawa wasu kantomomin riko a Jihar Bauchi, a maimakon gudanar da zabe kamar dokar kasa. Ya ce, Muna kira ga majalisar dokokin Jihar Bauchi da ta dauki mataki akan wannan kama-karya da mulkin soja da ake yi a jihar,i in har talakawa suke wakilta, domin bukatar mu ita ce a gudanar mana da zabe kamar yadda doka, ya haramta nada kantoma a karamar hukuma.
Yau kananan hukumomin Jihar Bauchi suna cikin mummunan halin kuncin rayuwa tunda karamar hukuma ba ta iya aikin da ya kai N50,000, ga talakawa duk dai a sakamakon rashin gwamnatin dimokuradiyya a kananan hukumomin.
’Yan majalisun dokokin Jihar Bauchi kusan da cewa  bambancin da ke tsakanin mulkin soja da na dimokuradiyya fa shi ne gudanar da zabe, kuma zabe ne ya kawo ku majalisa ka da ku amince da Kama karya, amma a Jihar Bauchi Kusan  angulu da kan zabo ake yi mana a kananan hukumomin mu tamkar sojoji ne ke mulki

Daga Amadu Manager Daga Bauchi Unguwan Karofin Madaki a Najeriya.08065189242.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya