Yaushe za a warware sabanin ganin wata?

A ranar Lahadin wancan makon wato 27-07-14, wasu al`ummar Musulmin kasar nan suka yi Idin Sallah karama, bayan sanarwar ganin sabon jinjirin watan Shawwal da mai alfarma Sarkin Musulmi,  Alhaji Muhammad Sa`ad Abubakar, kuma shugaban Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci na kasa baki daya, ya bayar ta kafofin yada labaran kasar nan a cikin […]

Yaushe za a warware sabanin ganin wata?
Yaushe za a warware sabanin ganin wata?

A ranar Lahadin wancan makon wato 27-07-14, wasu al`ummar Musulmin kasar nan suka yi Idin Sallah karama, bayan sanarwar ganin sabon jinjirin watan Shawwal da mai alfarma Sarkin Musulmi,  Alhaji Muhammad Sa`ad Abubakar, kuma shugaban Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci na kasa baki daya, ya bayar ta kafofin yada labaran kasar nan a cikin daren Asabar. A bana dai an ga watan na Shawwal a jihohi 10, na Arewacin kasar nan, wadanda suka hada da Kano da Katsina da Adamawa da Zamfara da Neja da Sakkwato da Jigawa da Kaduna da Kebbi da Barno.
Duk da yawan jihohin da aka samu bayanin ganin watan na Shawwal, a banan ma sai da aka samu sabanin yin Sallah karamar tsakaninmu da `yan uwanmu na Kudancin kasar nan, wadanda su ba su yi Sallar ba a ranar Lahadi, sai kashegari wato Litinin. Kai koda a nan arewar, a banan ma sai da aka kwata abin da yake faruwa duk shekara, musamman a kauyuka, yadda ba su fara azumi a ranar Lahadi bisa ga sanarwar da Sarkin Musulmi ya bayar ta ganin watan na Ramadan haka ma ba su ajiye ba, su yi Sallah ranar Lahadi, wannan ta sanya wasu har sai ranar Talata suka yi tasu sallar.
Kai! ta kai ma fagen da wasu ke cewa kasar nan a duk kasashen duniyar Musulmi ita ce kan fara ganin watan Ramadan, haka ma wajen ajiye azumin bisa ga ganin watan Shawwal. Amma wannan ba hanzari ba ne, don kuwa addinin Islama bai ta`allaka ganin watan wata kasa akan na wata ba. Babban abin da ya ta`allaka shi ne ganin watan mutane uku adalai, wadanda ganinsu kan lizamta wa saura su dauka ko su ajiye azumi. Hadisin Manzo SAW ya tabbatar da cewa Balaraben kauye ya zo wajen Manzo SAW, da jawabin ya ga watan Azumi, wanda bayan Manzo SAW, ya gasgata imaninsa ya bada umurnin sauran al`umma su dauki azumi. Ka gani mai karatu ganin wata ba wata daraja ko mu`ujiza ba ce da Allah Ya kebe ga wasu salihan bayinSa, don kuwa da a zamanin Manzo SAW, da ba wanda zai ga wata sai Shi ko SahabbanSa.
Dadin dadawa, mu a kasar nan har tsayayyen Kwamiti ake da shin a ganin wata a karkashin kulawar Mai alfarma Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Waziri Junaidu yake babban Sakatarensa na kasa, wanda ke bin diddikin tsayawa da karewar dukkan watannin addinin islama. Kwamitin yakan samu rahotannin tsayawa da karewar kowane wata daga kananan Kwamitocinsa na kowace Majalisar Masarautar addinin Islama da ke kasar nan duk wata, amma don kawai a shiga rudani sai ka taras a lokacin ganin tsayuwa da karewar watan Ramadan kawai rudani ke shigowa, ya kuma raba kawunan al`ummar musulmin kasar nan. Bugu da kari kuma mene ne abin rudani, akwai ranar da aka ce an ga watan azumi (Ramadan) alhali watan Sha`aban yana 28, ko akwai ranar da aka taba cewa an ga watan Shawwal, alhali  Ramadan na 28? Babban abin da karantarwar sunnah Manzo SAW ta tabbatar shi ne wata 29 ko kuma 30, wasu Maluman ma suka ce mafi yawan kwanakin wata su ne 29.
Ya kamata mu duba yadda ake tantance ganin watan Ramadan (Azumi) a kasar nan. Mai alfarma Sarkin Musulmi da `yan uwansa sarakuna ba su ke ganin wata ba, koda sun gani, sukan jira a ji ta bakunanan talakawa, ta hannun wakilan Sarakunan, wato dagatai da masu ungunnnni.  Duk talaka ko talakawan da suka yi ikirarin ganin wata a garuruwansu ko ungunnunsu, sukan kai kansu gidan mai unguwarsu, wanda kan dauke su zuwa gidan dagaci, daga nan idan dagaci ya amince da jawabansu sai ya kwashe su zuwa Fadar Sarkinsu. A fada in sun je za su taras da Sarki  da fadawansa da wasu  manyan maluman. Maluman da bayan gabatar da masu ikirarin ganin watan gaban Sarki, Sarki ya yi masu `yan tambayoyin da yake so yakan barsu da Malumannan da za su fara da tabbatar da imanin masu ikirarin ganin watan, sannan kuma su ci gaba da yi musu tambayoyi, har ta a wace kusurwa suka ga watan sai an tambayesu, akasari kuma da dai-daya da dai-daya akan tammbayesu kome yawansu. Mai karatu ka gani ba da ka ba, ake samun sanarwar ganin watan Ramadan ko na Shawwal ba, watanni biyu da ake ta fama da samun rudanin ganinsu duk shekara a kasar nan.
Amma kuma wani hanzari ba gudu ba, a `yan shekarun nan a bisa ga amincewar mai allfarma Sarkin Musulmi Kwamitin ganin watan na kasa ya fara yin amfani da na`urorin kimiyya wajen ganin wata, wannan kuma ita ce hanyar da take kara banranta talakawa da Sarakunan. Ka dauki sanarwar a fara duba jinjirin watan Shawwal a bana da babban Sakataren Majalisar koli ta addinin Musulunci Farfesa Ishak Oloyede ya bayar a ranar Alhamis24-07-14, da ta ce a fara duba sabon watan daga ranar Lahadi, ranar da a rannan watan na Ramadan ya ke ciki kwanaki 30.
A cikin waccan sanarwa, da babban Sakataren ya sanya wa hannu ta fadi cewa kwata-kwata kar ma a nemi jinjirin watan na Shawwal a ranar Asabar da watan na Ramadan yake 29, domin a lissafinsu na kimiyya, wai tsakar dare Asabar din za a haifi jinjirin watan na Shawwal, don haka a yammacin Asabar din ba a ma halicceshi ba, bare a ce an ganshi da wannan yammaci. Ya kara da cewa koda a ranar Llahadi da watan na Ramadan yake ciki kwanaki 30, sai da na`urorin kimiyya za a iya ganin watan, ganin da idanu kuwa a ranar kuwa sai  da kyar da jibin goshi.
Kodayake Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kwamanda Janar na Hisbah a jihar Kano ya gyara masa kuskuran a duba wata a ranar wani watan na 30. Shi kanshi Sakataren Kwamitin ganin wata na kasa Farfesa Junaidu ya fadi daga baya cewa za a iya fara duba ganin sabon watan na Shawwal daga 29, ga Ramadan, abin da kuma ya zama an ga watan a yammacin Asabar a cikin wadancan jihohin Arewa 10.
Ina ga lokaci ya yi da Mai alfarm Sarkin Musulmi da sarakuna `yan uwansa za su rinka bari jama`ar Musulmin kasar nan su rinka yanke wa kansu hukunci, idan dai har suna son martabarsu ta dore a idanuwan talakawansu. Batun su dage akan sai mun yi aiki da ganin watan kasar Saudiyya ba daidai ba ne, don kuwa ba nassin Al`kuri`ani ko  Hadisin Manzo SAW ba ne. Ina ga yanzu daidai lokacin ya kamata Sarkin Musulmi da Kwamitin ganin wata na kasa ya kamata su dukufa waje fara aiki da sanarwar bayan taron warware takaddamar ganin wata da suka gabatar a Abuja tsakanin 16 zuwa 19 ga watan Yulin da ya gabata a Abuja, musamman kiran da aka yin a lallai a dukufa wajen ganin an kawar da rudani da shakku da ake samu wajen ganin wata, wanda ta hanyar  wayar da kan jama`ar Musulmi kawai hakan zai samu, tsarin da yanzu ba shi. Ina dai sake yi wa al`ummar Musulmi Barka da Sallah Allah Ya maimaita mana.