Yawaicin makarantun kasar nan ba su da malaman lissafi – Farfesa Garba
Wani Farfesan Ilimin Lissafi da ke Jami’ar Jos kuma wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Farfesa Emmanuel Garba ya ce duk da cewa ilimin lissafi shi ne kashin bayan kowane ilimi a duniya, yawaicin makarantunNajeriya ba su da malaman koyar da darasin ilimin lissafin. […]
Wani Farfesan Ilimin Lissafi da ke Jami’ar Jos kuma wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Farfesa Emmanuel Garba ya ce duk da cewa ilimin lissafi shi ne kashin bayan kowane ilimi a duniya, yawaicin makarantun
Najeriya ba su da malaman koyar da darasin ilimin lissafin.
Farfesa Emmanuel Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kungiyar Tsofaffin daliban Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi reshen Jihar Filato suka shirya a garin Jos.
Ya ce, “Za ka ga wadanda suke koyar da lissafi a makarantun kasar nan, ba masana ilimin lissafi ba ne, masana wasu fannonin ilimi ne daban. Don haka irin wadannan malamai da suke koyar da lissafi a makarantun kasar nan, ba sa koyar da shi yadda ya kamata.”
Farfesa Garba, ya ce: “Ilimin lissafi shi ne kashin bayan kowane ilimi a duniya. Domin ana amfani da lissafi a kowane fannin ilimi don haka dole mu ba da karfi kan wannan fanni na ilimi. kasashen da suka ci gaba suna karfafa wa dalibansu gwiwa wajen daukar fannin ilimin lissafi.
Don haka idan ana son yaranmu su rika daukar fanni ilimin lissafi to a rika ba su gurbin yin karatu a finnin ilimin lissafi kyauta a makarantun kasar nan.”
Farfesa Garba ya ce kamar a kasar Rasha, idan mutum zai yi karatun fannin ilimin lissafi ana ba shi gurbin karatu kyauta a makarantar da zai yi. Kuma idan ya gama za a ba shi aiki. Ya ce “Ya kamata mu yi koyi da wannan don mu karfafa wa yaranmu gwiwa wajen daukar fannin ilimin lissafi a kasar nan.”
Ya ce akwai matsaloli da dama a jami’o’in Najeriya da suka hada da rashin kayayyakin aiki da karancin ajujuwa, ta yadda ake samun dalibai sama da dubu biyu a aji daya a jami’o’in kasar nan.
Ya ce yanzu daliban jami’o’in Najeriya ana koyar da su karatu ne kawai, amma ba su samun damar yin abubuwan da suka karanta a aikace saboda matsalolin rashin kayayyakin aiki.
Farfesa Garba ya ce hanyoyin magance matsalolin su ne jama’a su fahimci cewa ilimi ya fi karfin gwamnati ta dauka ita kadai. Don haka dole ne a hada hannu da masu dukiya da kungiyoyin da bayar da tallafi ga harkokin ilimi domin a tallafa wa jami’o’in kasar nan.
Sai ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, kan burinta na bunkasa ilimi, musamman da ta ce a bana za ta debi malamai dubu 500 tare da gyara gine-ginan makarantu da samar da kayan aiki.
A jawabin Sakataren kungiyar Ambasada Pual Daniel ya ce sun shirya taron ne don su kara dankon zumunci a tsakaninsu, kuma su taimaka wa Jami’ar Abubakar Tafawa balewa tare da karrama manyan malamansu da suka koyar da su a jami’ar.
Ya ce malaman da suka karrama sun hada da Shugaban Jami’ar Abubakar Tafawa balewa Farfesa Saminu A. Ibrahim da Farfesa Emmanuel Garba na Jami’ar Jos da Farfesa danladi Salim Matawal da Farfesa Isaac S.R. Butswat da kuma Farfesa Y.P. Mancha.
Ya yi kira ga tsofaffin daliban da ke Jihar Filato su ba su hadin kai da goyon baya don su tallafa mata su kuma tallafa wa al’ummar jihar.