Yawaitar fyaɗe ga ƙananan yara a Arewa

Fyaɗe kullum ƙara yawa yake yi don a yanzu aƙalla mukan karɓi koke har guda 20 a rana.

Yawaitar fyaɗe ga ƙananan yara a Arewa

Fyade

Wata yarinya mai shekara 6 da aka sakaya sunanta, tana cikin wadanda aka taba yi wa fyade.

Mahaifiyarta ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda ta bayyana cewa, “Ita wannan yarinyar ita ce ta bakwai a cikin ’ya’yana.

“A wata ranar Lahadi da karfe 6 na yamma, na nemi yarinyar ban gan ta ba, na shiga ko’ina cikin gidajen makwabta ba a gan ta ba, sai zuwa wani lokaci ta dawo.

“Na tsare ta, ina tambayar ta inda ta je. Da na tsorata ta, shi ne ta fada min cewa, tsohon makwabcinmu ne ya saka ta a dakinsa na gefen gida, ya ba ta sukari, ya yi mata abin da ya yi mata.”

Ta ce, wannan mutum ana zargin sa a unguwar cewa, yana raba wa yara sukari ne domin ya yaudare su.

“Mun je Asibitin kwararru na jiha da yarinyar, an tabbatar an bata ta, kan haka muka kai maganar gaban hukuma,” inji ta.

Mahaifin yarinyar mai shekara 54 ya ce ya so ya dauki mataki mai tsanani kan lamarin, amma mutanen unguwa suka ba shi baki kan ya sassauta lamarin, shi ne ya amince amma da sharadin su yi yarjejeniya ba zai sake kula ’ya’yansa ba, duk da mahaifiyar yarinyar ba ta gamsu da wannan hukunci ba.

Wanda ake zargin, mai shekara 55 da ke aiki a wani otel ya ce, kazafi aka yi masa, “Wannan maganar karya ce, sun yi min kazafi ne domin ina da wata jikakkiya tsakaninmu, in har ina yi, Allah Ya tona asirina kada Ya ba ni abin da nake so duniya da Lahira.

“Maganar ina raba wa yara sukari, kyauta ce ba don wani abu ba. Ni ba zan taba aminta da abin da ban yi ba.”

Wata budurwa mai shekara 21, wadda tun tana ’yar shekara 10 wani mutum mai shekara 72 mai sana’ar wanki da guga a unguwarsu ya yi mata fyaɗe, abin da ya yi sanadiyyar ta ci gaba da ba shi kanta, har ta samu ciki, bayan mako biyu aka gane tana da juna biyu, inda aka bincika a asibiti, aka gano ya kai wata shida da shiga, yanzu ta haifi ’ya mace.

“Wata rana ce an aike ni, sai na shiga gidansa ba kowa, sai ya ba ni da na je nema wato abincin da ya lalace, kuma ba ni Naira 100 kyauta, ya ce gobe in dawo akwai shi, in dauka.

“Kullum idan na zo sai ya ba ni 100 a hakan har ya shige ni. Daga nan na riƙa kai kaina wurinsa, yanzu da hukuma ta shiga ciki, ya aminta zai aure ni, ni ma na yarda zan aure shi,” inji ta.

Kakar yarinyar mai kimanin shekara 60 ta yi da-na-sanin rashin yi wa jikarta kulawar gaske har wannan lamari ya rika faruwa tsawon shekara 10 ba ta sani ba, kuma ta aurar da yarinya da ciki, sanadin haka za ta auri tsoho don ya bata mata rayuwa.

Wata mai shekara 16 da aka yi wa fyade ta samu ciki har ta haifi yaro, inda shi ma hukuma ta shiga tsakaninsu kuma ya yarda zai aure ta.

Mahaifin yarinyar ya ce, matakin hukuma da muka dauka ne ya sanya wanda ya yi aika-aikar ya aminta zai aure ta, da alkawarin zama ne na Sunna ba cutarwa a tsakaninsu,

“Mun aminta da hakan,’’ inji shi. Akwai wata yarinya mai shekara 17 da maza hudu suka amince sun yi mata fyade.

Yayan yarinyar ne ya tsaya kai da fata cewa, ba za su bar maganar haka ba sai an kwato wa kanwarsa hakkinta.

Matsalolin da fyade ke haifarwa a tsakanin al’umma musamman tabarbarewar zamantakewa na yin illa ga ci gaban al’umma.

Alkaluman kididdigar fyade sun nuna cewa, a tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, an sami rahotannin fyade da yunkurin yin fyade har guda 93 a yankin Zariya.

A watan Yuni an sami fyade 25, sai yunkurin aikata fyade guda 12. Sai a watan Yuli an sami aikata fyade 14 yunkurin yin fyade 10, yayin da a watan Agusta aka sami fyade 22 sai yunkurin aikata fyade sau 10.

A zantawar da Aminiya ta yi da masana harkar shari’a kan wannan mummunar dabi’a, wata Lauya mai zaman kanta, Barista Aisha Ahmed ta yi bayanin cewa, fyade ba abu ne mai kyau ba, saboda illata yara ake yi, su taso cikin damuwa.

Ta ce, a mafi yawan lokuta, iyaye sukan boye bayanai wai a matsayin kariya ga mutuncin wadda aka yi wa fyaden, wanda hakan bai kamata ba.

Barista Aisha Ahmed ta kara da cewa, duk wadda aka yi wa fyade, an bata mata rayuwa, ko da kuwa mace ko namiji kuma yaro ko babba.

Haka kuma ta ɗora alhakin boye bayanai ba kan rashin sanin hakkin da ke tattare da aikata fyade da kuma tsoron abin da zai biyo baya ta fuskar shari’a.

Ta shawarci iyaye da su daina boye bayanai, su kuma rika sanar da hukuma a duk lokacin da aka sami rahoton fyade, domin a dauki matakin magance matsalar ta hanyar yin hukunci domin kiyaye aukuwar haka a nan gaba.

Da take bayani ta fuskar shari’a a game da hukunta wanda ya aikata fyade, Barista Aisha Ahmad ta ce, babu wata karamar kotu da ke da hurumin yin shari’a, ballantana ta bayar da belin wanda ake zargin ya ci zarafi ta hanyar yin fyade.

Ta ce, Babbar Kotun Jiha ce ke da ikon yin shari’a da kuma bayar da belin wanda ake zargin, shi ma ba da belin sai da kwakkwaran dalilai.

Ta ce, Jihar Kaduna ta yi gyarar doka kan fyade a 2020 a karkashin Final Kod da aka yi wa gyara.

Haka kuma wannan dokar ta tanadi hukunci ga duk wanda ya aikata fyade kamar haka: sashi na 258 (3) duk macen da aka samu da laifin yi wa yara fyade hukuncinta ya hada da kisa .

Shi kuwa namijin da aka samu da aikata fyade, za a hukunta shi ne a karkashin sashi na 258 (2).

Ita dokar ta tanaji hukuncin a yi masa dandaka sai kuma kisa, musamman in yaron ya yi kasa da sheara 14.

Sashi na 258 (4) na dokar ya yi tanadin yin dandaka da kuma daurin rai-da-rai idan wanda aka yi wa fyaden ya wuce shekara 14 da haihuwa.

Barista Aisha ta shawarci iyaye da su rika sanya ido a kan ’ya’yansu, musamman kananan yara domin kare su daga masu wannan muguwar dabi’a ta fyade.

Shi kuwa wani jagora a kungiyar fafuta kan kare hakkin al’umma ta Human Rights Network in Nigeria (HRNN) a yankin Birnin Tarayya Abuja, Kwamred Nura Muktar ya ce, babban dalili da yawanci ke jawo matsalar fyade shi ne sakaci daga bangaren iyayen yara.

Ya ce, dora wa yara talla ko tura su aikin aikatau a gidajen manya ko kuma barin su a karkashin kulawar ’yan aiki a gida tamkar na kai su ga fadawa wannan matsala, idan ba yi da ce ba.

Kwamred Nura Muktar ya ce, akwai kuma matsalar kulawar iyayen riko kamar kishiyoyi a maimakon hakikanin kulawar iyaye, sai kuma makarantu da a wani zubin ake samun alaka tsakanin dalibai da dalibansu mata.

Ya ce, a aikinsu ya hada da jagoranci wajen shigar da kararraki kan matsalar fyade a kotu a madadin yara, akwai kuma inda suka gano cewa, matsalar na aukuwa a tsakanin yara ’yan uwa da ke kadaita da junansu ba tare da an yi tunanin hakan na iya faruwa ba.

Ya bukaci iyaye da su rika kula da yaransu a dukkan wuri da suka samu kansu, don gudun fadawa tarkon.

Wasu iyayen wato miji da matarsa gabadayansu ma’aikata ne sai su wuce zuwa wurin aiki, su bar yaransu a karkashin kulawar ’yan aiki kamar masu gadi.

A nan ma a na fuskantar wannan matsalar. Ya ce, zafin takaicin fyade ga mace na zama a zukatan wasunsu tsawon rayuwa, har su koma ga Allah.

Wasu ba za su ji zafin abin ba sai a lokacin da suka girma za su ji zafin rabuwa da budurci gabanin zuwa dakunansu na aure.

Kodayake masana na cewa, akwai hanyoyi da dama da ke kai ga mace ta rasa budurcinta, amma dai wannan matsalar ce a gaba wajen kawar da shi, inda wata ba za ta san muhimmancinsa ba sai lokacin da ta yi aure.

Ya bukaci iyaye da su kara kaimi wajen kulawa da iyalansu, sannan idan matsalar ta auku, su yi tsayin daka wajen ganin an hukunta wadanda a ke zargi da hannu akai, a maimakon nuna sassauci ko neman sasanci ta bayan fage ko kuma watsi da shari’ar da sunan gudun bata sunan ’yarsu.

“Dole ne su hanzarta zuwa asibiti don tantace yarinya, bayan afkuwar hakan don samun takardar shaidar da za a yi shari’a da ita, sannan kuma su jajirce har zuwa matakin karshe a kotu,’’ in ji shi.

Laifuffukan da ke da alaka da fyade ga ’ya’ya mata su ne a kullum ke kara yawaita a tsakankanin jama’a, wanda hakan ke haifar da barazanar lalacewar al’umma, musamman matasa da su ne ke da kaso mafi yawa daga cikin kowace irin al’umma a kasar nan.

A rahoton da Aminiya ta samu na nuna cewa, ba komai ba ne ke haifar da ruruwar aikata wannan babban laifin ba a tsakanin al’umma a halin da ake ciki, illa wasu abubuwan da suka hada da sakacin iyaye da kuma uwauba sakacin da ake samu a mafi yawan lokaci daga hukumomin tsaro na rashin ladabtar da masu aikata wannan mummunan laifi na fyade ga kananan yara, wanda hakan ke ba su karfin gwiwar ci gaba da aikata irin wannan aika-aika.

Haka kuma in da a ce duk wanda ya aikata wannan laifi, yana fuskantar hukunci mai tsanani ba tare da sanin ko shi wane ne ko kuma dan wane ne ba, to kuwa da tunin labarin ya canza yadda ko an ce mutum ya aikata hakan, zai yi wa kansa fada, ya yi watsi da wannan ra’ayi.

Malam Babagana ya ce, wannan lamari na yawaitar aikata fyade da ake yi a cikin al’umma wanda ya zama ruwan dare, ya nuna cewa in da a ce hukuncin da gwamnatocin ke cewa sun sa ga duk wani wanda aka samu da laifin aikata fyaɗe ga wata mace, in ma yarinyar ce ko kuwa babbar mace da ana zartarwa bil-hakki da gaskiya, da tuni masu aikata irin wannan aika-aika sun yi watsi da aikata hakan.

Shi kuwa wani tsohon ma’aikaci a bangaren kiwon lafiya a Jihar Yobe, Malam Mamman Bello cewa ya yi, shi a ganinsa babu wadanda ke da ruwa da tsaki wajen dakile aikata irin wannan aika-aika ta fyaɗe illa iyaye, domin kuwa in da a ce iyaye mafi yawa suna sauke hakkokinsu, musamman ta wajen sa ido da bibiyar rayuwar ’ya’yansu mata tare da sauke nauyin da ke kansu da ya shafi ilimantar da su a fannin addini da na zamani, to kuwa da irin wannan lamari na aikata fyaɗe bai yawaita ba.

A cewarsa, amma matukar iyaye maza suka yi watsi da bibiyar yadda ’ya’yansu mata har ma da mazan ke tafiyar da rayuwarsu, to hakika wannan matsala ta fyaɗe ba za ta kau ba.

An danganta matsalar fyaɗe a Arewa da abubuwa masu sarkakiya ta bangarori da dama, lamarin da ya sa ake kira da a samar da cikakkiyar dabara don shawo kan lamarin.

A cewar Barista Fatima Raji, Shugabar Kungiyar Lauyoyin Mata ta Jihar Adamawa, tushen cin zarafin jima’i, musamman fyaɗe, a Arewacin Nijeriya ya shiga cikin al’adunmu.

Raji ta bayyana muhimman abubuwan da ke taimakawa da suka hada da rashin cikaken hukumci ga masu laifi da al’adu da zamantakewa da ke daidaita cin zarafin mata da ‘yan mata da rashin ilimi da wayar da kan jama’a da kuma rashin isasshen matakan tsaro da talauci.

“Dokar cin zarafin mutane ta 2015 mataki ne a kan hanyar da ta dace, amma aiwatarwa ya kasance babban kalubale,” in ji Raji.

Don yaƙar fyaɗe, Raji ta ba da shawarar samar da tsari mai ban sha’awa, tana mai cewa mai da hankali kan ilimi da haɗin gwiwar al’umma da tallafi ga waɗanda suka tsira da ƙaƙƙarfa aiwatar da doka da tsarin shari’a.

Lauyar ta jaddada cewa, aiwatar da tsarin dokoki za su taimaka sosai wajen dakile wannan mummunar dabi’a a tsakanin al’umma.

Ta ce, dole ne mu haɗa kai don samar da al’ummar da ba za a amince da cin zarafi ba kuma wadanda suka tsira a tabbatar da sun samun adalci da goyon baya.

Wasu jihohin Arewacin Nijeriya kuma sun kafa kotuna na musamman da za su gudanar da shari’ar cin zarafin mata.

Ita kuwa Malam Binta Buba mai bayar da shawara ce a Cibiyar Waraka da ke Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed, inda ta bayyana cewa, fyade na kara yawaita a Jihar Kano.

Ta ce, ‘’a gaskiya fyaɗe kullum ƙara yawa yake yi don a yanzu a kalla mukan karɓi koke har guda 20 a rana.

Wannan ma na wadanda suka iya fitowa da maganar ce, ban da wadanda ake rufe maganar ba tare da an kai gaban hukuma ba’’.

A cewarta laifin iyaye ne ya janyo hakan. Ta kara da cewa, ‘’Cibiyarsu ta Waraka ita ce wuri na farko da ake kai yaran da aka yi wa fyade.

“Kasancewar cibiyarmu ta hada da likitoci da masu bayar da shawarwari da kuma masana shari’a.

“Da zarar an kai wa ’yan sanda rahoton faruwar fyade sukan dauko yaran, su kawo mana.

“A nan muke duba cewa ko an yi fyaden ko akasin haka.

“Idan an yi fyaden za su bayar da gwajegwajen da za a yi wa yarinyar na HIV da wasu cututtukan da ake iya dauka.

“Daga nan mu kuma za mu zaunar da su don yi musu tambayoyi tare da kwantar musu da hankali a kan al’amarin gaba daya.

“Kafin daga bisani kuma mu damka su ga ’yan sanda don kai su kotu.

“Haka kuma idan su wadanda aka yi wa fyaɗen ne suka zo da kansu cibiyarmu ba tare da ’yan sanda ba, mukan saurare su tare da yi musu duk abin da suke bukata sannan mu hada su da ’yan sanda ko Kungiyar Mata Lauyoyi ta Kasa (FIDA) don taimaka musu’’.

Malama Binta ta dora laifin faruwar fyaden da ake yi wa yara a kan iyaye.

Ta ce, ‘‘akwai wata yarinyar da kakarta ce ke rikon ta, tana yi mata talla idan ba a samu na tallan ba to babu abinci don haka yarinyar ta rika tafiya yawo daga nan sai wayar gari aka yi yarinyar ta yi ciki.

Baya ga wannan kuma akwai yaran da suke fadawa kangin fyade sakamakon iyayensu ba su iya daukar nauyinsu.

“Idan aka duba za ku ga yara ƙananan suna kan titi, suna roko da sunan neman abinci.

“Akwai yarinyar da na gani tana goge gilashin mota wani direba ya ba ta lambar wayarsa wai ta kira shi.

Don Allah wace alaka yake kokarin kullawa a tsakaninsu’’.

A cewarta, ‘‘ba wai yara mata kawai ake yi wa fyade ba, har ma da maza.

“Domin su ma ana yin amfani da talaucinsu ana bata musu rayuwa. A wasu lokutan ma sai mu yi mako guda muna samun korafi kan cin zarafin ’ya’ya maza.

“Wallahi wani yaron ma ba sai an gwada shi ba, kina ganin yanayinsa za ki gane an ci zarafinsa, domin wasu da yawa ba su iya zama daidai ba’’.

Da take bayani game da hanyoyin da za a bi wajen magance ko rage yawan faruwar fyaɗe, Malama Binta ta ce lamari ne da ake bukatar sa hannun kowa da kowa.

‘’Da farko za a saka malamai don yin wa’azi a kan girman laifin fyade da zina gaba daya.

“Sannan a ci gaba da wayar wa iyaye kai wajen kulawa da ’ya’yansu. Dole ne iyaye mu ja ’ya’yanmu a jikinmu. Mu ba su kulawa kamar yadda muke kula da jakarmu da kuma wayoyinmu na hannu.

“Mu riƙa zaunar da su, muna gaya musu yadda za su guje wa masu neman lalata da su.

“Idan sun dawo makaranta, mu rika bincikarsu, muna tambayar su abin da ya faru da su. A sa wa ’ya’ya ido sosai’’, in ji ta.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos