Yawaitar fyade ga kananan yara na jefa tsoro a zukatan iyaye
Karamin hukuncin da za a yanke wa mai fyade shi ne daurin shekara 14 a gidan yari.
Matsalar fyade da ake yi wa kananan yara matsala ce da ta dade tana damun al’umma wacce kuma har zuwa wannan lokaci hukumomi da sauran masu ruwa-da-tsaki sun kasa shawo kanta.
A da wannan matsala tana faruwa ne a unguwanni da makarantu inda za a samu masu yin fyaden ba ’yan uwa na jini ba ne ga yaran, sai dai yanzu ana samun wannan mummunan lamari a tsakanin ’yan uwa na jini a wasu lokuta ma har ana samun mahaifan yara suna haka.
Wani abu da yake ba mutane mamaki shi ne yadda ake yi wa yara kusan jarirai fyade maimakon ’yan mata, wadanda ake zargi da shigar jan hankali lamarin da mutane da dama suke ganin karshen zamani ko tsafe-tsafe ne suke kawo haka.
Misalan fyade masu banmamaki
Ko a ’yan shekarun baya sai da ’yan sanda suka kama malaman wata makaranta su tara a Unguwar Rijiya Hudu bayan da aka samu gawar wata yarinya da aka yi wa fyade.
An dai gano gawar yarinyar ce a cikin ajin makarantar bayan kwana hudu da iyayenta suka sanar da bacewarta.
An ce an gano gawar har ta fara rubewa kwance a cikin jini kuma tsirara.
Haka kuma, a wani lokaci an zargi wani matashi dan shekara 26 mai suna Muhammad Suleiman, wanda malamin makaranta ne ya yi wa wata yarinya ’yar shekara uku fyade, bayan da ya yi mata wayo ya kai ta cikin wani aji.
Lamarin ya faru ne a Unguwar Rimin Gata da ke Karamar Hukumar Ungoggo a Jihar Kano.
Malamin yana fuskantar tuhuma a gaban wata kotun majistare a Kano kan laifin yin lalata da karamar yarinya.
Sai dai kuma, da aka gabatar da Muhammad Sulamain a gaban kotu kan zargin ya musanta yin lalata da yarinyar, inda ya bayyana wa alkali cewar sam bai aikata abin da ake zarginsa da shi ba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya an samu wani mahaifi da ya yi wa ’yar cikinsa fyade inda ya dora alhakin faruwar abin a kan aljanunsa wanda ya ce su suke sa shi aikata irin wadanan al’amura.
Duk da cewa dimbin matsalolin fyade da ke gaban kotuna suna jiran hukunci a Kano, an sake yi wa wata yarinya ’yar shekara bakwai fyade, abin da har ya so ya gusar da hankalinta.
Mahaifiyar yarinyar ta nemi a yi wa ’yarta, wadda marainiya ce, adalci da yake batun yana gaban kotu.
Yayin da wasu masana ke danganta dalilin yawaitar fyade ga kananan yara ga sakacin iyaye wasu kuma suna danganta shi ga yin halin ko-in-kula daga al’umma.
Kuma wasu suna ganin cewa marasa tsoron Allah suna aikata fyaden ne a dalilin neman abin duniya saboda bokayensu sun fada musu cewa sai sun yi wa kananan yara fyade sannan za su samu biyan bukatunsu.
‘Akwai laifin kafofin sadarwa’
Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum ya danganta lamarin ga yawan yayata labarin aukuwar fyade da kafafen watsa labarai ke yi a kowane lokaci.
“Da zarar an samu labarin faruwar fyade sai ki ga kafafen watsa labarai suna yayatawa.
“To a nan wanda ma bai san harkar ba sai ki ga ya nemi ya gwada aikatawa. Wannan ma babbar matsala ce,” in ji shi.
Wata mata mai suna Hajiya Sa’a Lawan ta bayyana matsalar fyade da cewa rashin aikin yi ga matasa ne wadanda kuma suna bukatar aure ke janyo ta.
Ta ce, “Matasa ne sun shiga shekarun balaga suna bukatar aure ga shi kuma ba su da sana’ar da za su dauki dawainiyar iyali hakan ya sa suke ci gaba da yi wa kananan yara fyade.”
A cewarta dole sai iyaye sun tashi tsaye sun sa ido a kan shige da ficen ’ya’yansu.
“Su sani cewa ’ya’yan da Allah Ya ba su amana ce kuma zai tambaye su yadda suka tafiyar da sha’aninsu.
“Dole ne a matsayinki na uwa ki daina sakin ’yarki sasakai. Ma’ana ya kansance a koyaushe tana jikinki a gida.
“Ki daina aiken ta musamamn a lokutan da aka san babu mutane a unguwa.
“Haka idan akwai maza da ke gidan ki rika janye ta daga gidan domin yawanci masu yi wa yaran nan fyade ’yan uwansu ne na jiki,” in ji ta.
Lamarin akwai daga hankali — Barista Bilkisu
Duk da cewa hukumomi suna cewa suna abin da ya kamata wajen dakile wannan matsala, sai dai kuma har yanzu ana ci gaba da samun wadannan matsaloli, wadanda a cewar wata lauya mai fafutikar tsaya wa wadanda ke fuskantar shari’a kan cin zarafi, kuma Shugabar Kungiyar Mata Lauyoyi ta Kasa, Barrista Bilkisu Sulaiman abin damuwa ne.
A cewarta kungiyarsu tana kokarin wayar da kan al’umma a kan abin da ya shafi fyade musamman game da yadda iyaye za su kiyaye tare da ganin cewa ba a yi wa ’ya’yansu fyade ba.
“A matsayinki na uwa ki tabbatar ba ki yi wa ’yarki kowane irin aike a wasu lokuta ba misali a lokacin da dukkan mutanen unguwa ba su nan, irin ranar Juma’a lokacin tafiya masallaci.
“Haka akwai bukatar iyaye su sa ido tare da sanin halin da ’ya’yansu suke ciki.
“Ki ja ’yarki a jiki yadda da zarar wani abu ya same ta za ki yi saurin ganewa.
“Idan kika ga wani canji a fuskarta ko a yanayinta sai ki yi saurin bincikawa.
“Kai idan ma kika yi sa’a da kanta za ta fara sanar da ke abin da ke damunta.
“Haka muna fada wa iyaye su rika hana ’ya’yansu kwadayi tare da fada wa ’ya’yan cewa su sanar da su game da duk wanda yake yi musu wasa ko kyauta a ko’ina don hakan zai taimaka musu wajen gano mutanen da ke bibiyar ’ya’yansu,” in ji ta.
Ta kara da cewa, “Kungiyarmu tana tsaya wa duk yarinyar da aka ci zarafinta ta hanyar fyade tun daga matakin unguwa har zuwa asibiti don yin gwaji don tabbatar da cewa an yi fyaden ko ba a yi ba.
“Idan muka samu gamsasshen bayanin likita a kai sai mu wuce wurin ’yan sanda inda za a dauki bayanai har da na wanda ake zargi daga nan a zarce kotu har zuwa lokacin da za a zartar wa mai laifi hukunci.
“Mun ji dadin yadda a yanzu aka fitar da hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin fyade to karamin hukuncin da za aiya yi masa shi ne daurin shekara 14 a gidan yari.”
Sai dai ta koka game da rashin hadin kai da suke fuskanta daga iyayen yara.
“Duk da cewa muna wayar musu da kai cewa idan an yi fayde kada a yi saurin wanke jikin yarinya kafin a kai ta asibiti, amma sai mu ga ba su ji, ba su yin aiki da abin da ake fada musu.
“Haka ba su ba mu hadin kai wajen bin lamarin a kotu har zuwa karshe.
“Da an fara sai ki ga sun daina zuwa kotu suna cewa wai su sun bar wa Allah.
“To wanda ke da lamari ya janye kai kuma babu abin da za ka iya yi a kai. Wannan shi ne babban kalubalenmu,” in ji ta.
Shugabar ta koka game da abin da ta kira rashin wayar da kai daga bangaren gwamnati, inda ta yi korafin cewa cibiyar da ke duba wadanda suka hadu da matsalar wato WARAKA ta yi kadan a jihar.
Ta ce, “Kin ga irin wannan cibiya ta WARAKA duk sauran jihohin suna da su sama da daya, amma a Kano daya tal muke da ita, ita ma din tana cikin wani hali marar kyau.
“Domin gwamnati ta cire hannunta a kai, haka kungiyoyi masu zaman kansu sun janye tallafin da suke ba cibiyar.
“Yanzu haka cibiyar tana nan sai dai mutane ne ke taimakawa da kai dauki a duk lokacin da ka samu irin wannan.”
Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura kasancewar ya yi alkawarin zai tuntubi wakiliyarmu don ba ta cikakken bayani a kan lamarin sai dai kuma hakan bai samu ba, har zuwa hada wannan rahoto.