Yawaitar hadari a manyan hanyoyin Najeriya

A makon jiya ne Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar da rahoton da ke nuna yawaitar adadin mutanen da ke rasa rayukansu sanadiyyar haddura a manyan hanyoyin kasar nan. Rahoton da aka fitar a Abuja na bayyana cewa ’yan Najeriya 1,331 da suka rasu sanadiyyar haddura a hanyoyin kasar cikin wata uku.  Rahoton ya […]

Yawaitar hadari a manyan hanyoyin Najeriya
Yawaitar hadari a manyan hanyoyin Najeriya

A makon jiya ne Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar da rahoton da ke nuna yawaitar adadin mutanen da ke rasa rayukansu sanadiyyar haddura a manyan hanyoyin kasar nan. Rahoton da aka fitar a Abuja na bayyana cewa ’yan Najeriya 1,331 da suka rasu sanadiyyar haddura a hanyoyin kasar cikin wata uku. 

Rahoton ya ce, mutum 1,257 daga cikin 1,331 da suka rasun matasa ne sauran 74 yara ne kanana. An bayyana ’yan Najeriya 8,437 da suka samu raunuka a hadarin na wannan lokaci.

Rahoton ya ce, ’yan Najeriya 6,415 maza na wakiltar kashi 76 cikin 100 wadanda suka samun raunuka sakamakon haddura a hanyoyin kasar nan a rabin shekara kamar yadda mata 2,022  da ke wakiltar kashi 24 cikin 100 na wadanda suka samu raunukan.

Duk da irin suka da shirin gyaran hanyar ke fuskanta a hanyoyin kasar, har yanzu muna da rahoton asarar da ake samu a hanyoyin. ’Yan Najeriya 1,331 ne suka rasa rayukansu a hanyoyin  cikin wata uku kamar yadda rahoton ya gabatar. Muna jajanta wa iyalan wadanda suka rasa ’yan uwansu, wadanda suka samu raunuka muna yi musu fatan saurin samun sauki. 

Don haka akwai bukatar bin hanyoyin da za a kiyaye haddura, muna jinjina wa Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) kan kokarinta na kiyaye hadurra a hanyoyin kasar, muna bukatar ta ci gaba da kokari fiye da yadda take yi har sai an samu raguwar haddura a kasar nan.

Kamata ya yi Hukumar FRSC ta gudanar da gangamin ilimantar da direbobi da masu amfani da hanyoyi a kasar nan. Akwai bukatar a sanya alluna da alamomin a kan hanyoyi musamman hanyoyin da suka lalace da kuma wadanda ake gyarawa da wadanda ake ginawa, wannan zai zama gargadi ga direbobin.

Bugu da kari, maimakon jami’an Hukumar FRSC su zauna a cikin manyan garuruwa kamata ya yi su fita zuwa manyan hanyoyin da aka fi hada-hada da ababen sufuri inda aka fi bukatarsu.

Kamata ya yi jami’an Hukumar FRSC su samar da wani hukunci ga masu saba dokokin hanya. Da kuma kara hukunta masu laifi ta hanyar kara musu tara saboda taka doka da suka yi. A sanya wadansu mutane su biya don ya zama gargadi ga masu aikata laifuffuka.

Jami’in binciken motoci ya kasance yana gudanar da ayyukansa kamar yadda ya dace. Su tabbatar da ingancin duk motar da za ta bi hanya, saboda wasu hadduran na faruwa sanadiyyar rashin kyan taya. Jami’an su kasance masu duba kwanan watan tayoyin motoci da ke bukatar canji sannan a tsare duk direban da ya bi hanya da irin wadannan tayoyin, kuma a rike motar har sai direban ya sayi sababbin taya kafin a ba shi motarsa. Hanyoyin da dama a fadin kasar suna cikin matsalar lalacewa, yanzu haka matsalar ta yi kamari saboda lokacin damina da aka shiga. Don haka muna kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihoh su tabbatar da suna gyara hanyoyin don kauce wa haddura.

Wasu hanyoyin kasar nan kamar tarkon mutuwa ne. Bai dace a ce Najeriya ta ci gaba da asarar ’yan kasarta ba, saboda sanadiyyar abubuwan da aka ki jini. Akwai bukatar a sa himma wajen gyara lalatattun hanyoyin kasar nan a duk fadin kasar wanda hakan zai zama alfaharin Gwamnati.

Kuma a lura magance matsalar gwamnati kadai ba za ta iya ba. Sai mun hada gwiwa wajen kiyaye hanyoyin kasar nan. Hakan zai canja dabi’un direbobi.  

Rahoton ya bayyana cewa, yawan gudu da ababen hawa na kawo haddura da wasu direbobi ke yin sanadi, wanda hakan mummunar dabi’a ce.

Da gaske ne hanyoyi da dama ba su da kyau, amma idan direbobin suka yi hattara hadduran ba za su kai adadin da ake samu a yanzu ba. Akwai matsalar karancin shekaru ga wadansu direbobi da ke tuki. Iyaye na bukatar su san cewa akwai ’ya’yansu da ba su kai shekarun da ya kamata su fara tuki ba, matsalar ba kawai za ta kare a kan direba ba ne har takan shafi wadansu. Don haka ya kamata su kiyaye aukuwar haka. A kauce wa tuki lokacin da aka sha giya ko wasu kwayoyin maye. Mai hankali wanda aka horar ne ya kamata ya zama direba. Kiyaye haddura a kasar nan ya rataya ne a kan wuyan kowa.