Yawaitar mace-mace: Kwankwaso ya nemi Buhari ya kai dauki

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kai wa jihar Kano dauki game da annobar mace-mace da ta jefa al’umma cikin zullumi. A wata budaddiyar wasika da ya rubuta ga shugaban kasar, Kwankwaso ya bayyana damuwa game da halin da al’ummar jihar suka shiga. inda […]

Yawaitar mace-mace: Kwankwaso ya nemi Buhari ya kai dauki

Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kai wa jihar Kano dauki game da annobar mace-mace da ta jefa al’umma cikin zullumi.

A wata budaddiyar wasika da ya rubuta ga shugaban kasar, Kwankwaso ya bayyana damuwa game da halin da al’ummar jihar suka shiga. inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta yin abin da ya dace a kan lokaci kafin abubuwa su kazanta.

Tsohon gwamnan ya dora alhakin yawaitar mace-macen a kan rashin kwararru a cikin kwamitin da ke yaki da cutar coronavirus a jihar.

Ya ce yanzu haka cibiyar gwaje-gwaje da ke Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano tana garkame saboda rashin kayan aiki.

Hakan, a cewarsa, ya jawo cutar tana kara yaduwa a tsakanin al’ummar Jihar.

“Yadda daruruwan manyan mutane suka mutu a makwanni biyu da suka wuce abin dubawa ne ga duk mai hankali.

“Duk da an ce wasu daga ciki da ma sun yi fama da rashin lafiya, akwai bukartar gwamnatin tatayya ta sa wasu kwararru da za su je makabartu don tattara bayanan wadanda suka mutun don gano musabbabbin mutuwar tasu tare da bibiyar dukkanin wadanda suka yi mu’amala da gawarwakin don yi musu gwaji tare da killace su”, inji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samar da cibiyoyin gwaje-gwaje akalla guda biyar da kuma cibiyar karbar samfurin jini akalla guda 10 a fadin jihar.

Ya kuma nuna takaicinsa game da siyasantar da rabon tallafin da gwamnatin jihar Kano ke yi inda ya yi zargin cewa ana zaben mutum hudu daga kowacce rumfar zabe mai mutane 500.

“Babu yadda za a kulle mutumin da yake jin yunwa a gida wanda yake samun abincinsa a kullum bayan ba ka yi masa wani kyakkyawan tsarin samun tallafi ba, don haka muke neman gwamnatin tarayya ta rubanya tallafinta yadda zai kai ga kowa a jihar”, inji tsohon gwamnan na jihar Kano.

A ‘yan kwanakin nan dai an samu mace-mace da yawan da hatta masu kula da makabartun birnin Kano suka ce ba su taba ganin  irin su ba.

Gwamnatin jihar dai ta ce wadannan mace-mace ba su da alaka da cutar coronavirus.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu