Yawaitar wayoyin tarho marasa inganci na ci wa Hukumar NCC tuwo a kwarya

Ta wallafa wayoyin tarhon da ta amince da su a shafinta na yanar gizo Saboda damuwar da ta yi da ci gaba da yawaitar jabun wayoyi da kayayyakinsu a kasar nan, Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta sake shawartar masu amfani da wayoyin tarho su nisanci sayen wayoyin tarho da kayayyakinsu da ba su da […]

Yawaitar wayoyin tarho marasa inganci na ci wa Hukumar NCC tuwo a kwarya

Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta

  • Ta wallafa wayoyin tarhon da ta amince da su a shafinta na yanar gizo

Saboda damuwar da ta yi da ci gaba da yawaitar jabun wayoyi da kayayyakinsu a kasar nan, Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta sake shawartar masu amfani da wayoyin tarho su nisanci sayen wayoyin tarho da kayayyakinsu da ba su da inganci.

Wannan shi ne muhimmin abin da aka tattauna a taron yini daya kan hadarin amfani da jabun wayoyin tarho da yadda suke shafar ingancin sadarwa, wanda aka gudanar a garin Paiko da ke Jihar Neja kwanakin baya.

A jawabin Shugaba kuma Babban Jami’in Hukumar NCC, Farfesa Umar Dambatta ga mahalarta taron wanda aka yi tambayoyi tare da bayar da amsoshi a tsakanin abokan hulda da masu sanya ido, ya ce  shirin wayar da kan yana daya daga cikin kokarin da hukumar ke yi na ilimantarwa da wayar da kan al’umma kan hadarin yin amfani da jabun wayoyi da ba su da inganci da kuma  yadda suke shafar tattalin arziki.

Dambatta wanda Daraktan Shiyya na Sashen Ayyuka na Hukumar NCC, Malama Amina Shehu ta wakilta ya bayyana cewa “Shiri ne da hukumar ta tsara don ilimantarwa da wayar da kan jama’a kan  wayoyin da hukumar ta amince da su da alfanun yin amfani da kayayyakin wadanda suka hada da samar da ingantacciyar sadarwa da bayar da kariya ga masu yin amfani da su.”

Amina Shehu wacce ta nuna damuwa kan yawaitar jabun wayoyi a kasar na ta ce jabun wayoyi sun zama ruwan dare da ke bukatar a ilimantar da masu amfani da su da hada gwiwa a tsakanin ma’aikatun gwamnati don magance matsalar. Ta bukaci masu amfani da wayoyin tarho su binciki shafin yanar gizon hukumar don ganin jerin sunayen wayoyin da aka amince da su sai su zaba su saya.

“Yawaitar amfani da jabun wayoyin ya zama ruwan dare a kasashe masu tasowa kamar Najeriya inda masu shigo da kaya suke kawo jabun wayoyin ba tare da la’akari da wayoyin da aka amince da su ba,” inji ta.

Ta ce dokar shekarar 2003, sashe na 132 ta bai wa hukumar ikon kafawa da tilasta yin amfani da kayayyakin sadarwa masu inganci a Najeriya don tabbatar da sun yi aiki mai inganci a harkar sadarwa.

Saboda haka dukan masu kera irin wadannan kayayyaki da masu sayar da su da kamfanoni har da masu amfani da su kamar wayoyin tarho su tabbatar kayayyakinsu sun dace kafin a shigo da su Najeriya. Ta ce Hukumar NCC tana da alhakin tabbatar da abokan hulda suna taka rawa a masana’antar sadarwar.

Amina ta ce hukumar da hadin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro da wasu ma’aikatun gwamnati kwanakin baya sun kaddamar da kwamitoci biyu don tsara yadda za a dakile yawaitar jabun wayoyi a kasar nan.

Ta  ce hukumar ta tsara ka’idoji kan kayayyakin lantarki wadanda za su samar da tsarin sanya ido wajen tattalin kayayyakin lantarki a masana’antar sadarwa da suke kan tsarin sashe na 132 na dokar hukumar ta shekarar 2003.

Da yake jawabi a madadin masu amfani da kayayyakin sadarwa da mahalarta taron, Hakimin Paiko, Alhaji Mansur Baba Mustapha ya yaba wa hukumar saboda kawo shirin zuwa garin Paiko.

Ya yi korafin raunin tsarin sadarwa, da  sakonnin da kamfanonin waya ke turo musu wadanda ba su nema ba, inda hukumar ta amsa da cewa akwai bukatar shiga tsarin lambar 2442 don dakatar da sakonin.