Yawan abokan shafin facebook sun zama kudin kwanan otal

Otal din alfarma na Nordic Light Hotel da ke Stockholm, babban birnin kasar Sweden, ya bayar da sanarwar zai bayar da wurin kwana kyauta ga duk mutumin da ke da abokan hulda a shafukan facebook, wadanda yawansu ya haura dubu biyu. Mutanen da ke da abokan hulda a shafukan facebook da suka kai dubu 100, […]

Yawan abokan shafin facebook sun zama kudin kwanan otal
Yawan abokan shafin facebook sun zama kudin kwanan otal

Otal din alfarma na Nordic Light Hotel da ke Stockholm, babban birnin kasar Sweden, ya bayar da sanarwar zai bayar da wurin kwana kyauta ga duk mutumin da ke da abokan hulda a shafukan facebook, wadanda yawansu ya haura dubu biyu. Mutanen da ke da abokan hulda a shafukan facebook da suka kai dubu 100, za su yi kwana bakwai ba tare da sun biya kudi ba, amma za su aike da sakonnin talla a shafukansu.
Marcus Majewski, wanda shi ne shugaban sashe gudanarwa a otal dinThe Nordic Light Hotel, ya ce a harkar hada-hadar kasuwanci, su sun dauki sakonni da ake aikewa a shafukan sadarwa a matsayin ”kudi” don suna tallata hajar otal din.
“Ina alfaharin ganin cewa otal din mu ne na farkoa wannan yankin da ya fara hada-hadar kasuwanci da irin wadannan “kudin,”acewar Majewski.
Otal din ke karbar kudin kwanan daki akan Dala 360, kowane kwana guda, ya fara rage farashinsa ga masu abokan da ba su wuce dubu biyu ba. Wadanda ke da abokan facebook 500 za a zaftare musu kaso biyar cikin100, inda za a rage kashi10 cikin100 ga masu abokai dubu.