Yawan Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza sun haura 7,000
Sai dai isra’ila ta ce har yanzu ba ta fara kai hari ta kasa ba ma tukunna
Hukumar Lafiya ta Zirin Gaza ta ce yawan Falasɗinawan da suka mutu sanadin hare-haren Isra’ila yanzu sun haura 7,000.
Kazalika, Hukumar Kula da Ayyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ta sanar a ranar Alhamis cewa kaso 68 na mutanen da aka kashe mata ne da kananan yara.
- Gwamnatin Legas ta kwace sama da motoci 100 da suke kwana a kan gadoji
- MDD za ta dakatar da aikin agaji a Gaza saboda rashin mai
Hukumar dai ta ce ta samu alkaluman ne daga kungiyar Hamas da ke mulkin Zirin na Gaza.
Kusan mutum 1,600 ne kuma kawo yanzu ake tunanin sun bace ɓat a yankin.
Sai dai har yanzu hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a yankin na sama ne, inda ta ce tana nan tana shirin kaddamar da wani ta kasa.
Tun a ranar bakwai ga watan Oktoba ne dai Hamas ta kaddamar da hare-haren a kan Isra’ila, kafin ita kuma ta mayar da martani.
Isra’ilar dai ta ce hare-haren na Hamas sun kashe mata mutane sama da 1,400, sannan aka yi garkuwa da sama da 222 ta karfin tsiya.
Sai dai daga bisani an saki hudu daga cikin Yahudawan da aka kashe.