‘Yawan hanyoyin shigowa Nijeriya na ƙara matsalar tsaro a ƙasar’
Musa ya ce hakkin tabbatar tsaro al’amari ne da ya shafi kowa da kowa.
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya jingina karuwar matsalar tsaro da ake fuskanta da yawaitar hanyoyin shigowa ƙasar ta barauniyar hanya.
Ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tattaunawa kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya wadda Cibiyar Bincike da Horaswa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta shirya.
- An sako wadda aka yi kuskuren ɗaure ta bayan shekara 43 a kurkuku
- Abin da ya sa muka dawo daga rakiyar zanga-zanga — Gamji
A cewarsa, Nijeriya tana da iyakoki 364 da kasa da kasa suka amince da su yayin da akwai haramtattun hanyoyi 1,497 da ake shigowa cikin kasar ba bisa ka’ida ba
Ya ce har ilau Nijeriya tana daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan yarjejenita Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS da ta haramta shige da fice ba tare da takardu izinin shiga kasashen ba.
Babban Hafsan ya kuma bayyana karanci jami’ai a bangaren tsaro a jerin manyan kalubalen tabbatar da tsaro a Nijeriya.
Haka kuma, babban jami’in tsaro ya alakanta tabarbarewar bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma rashin samar da ababen more rayuwa a matsayin sauran dalilai da ke kara ta’azzara lamarin a kasar.
Da yake bayyana matakan da ya kamata a dauka domin yi wa tufkar hanci, Janar Musa ya ce dole ne gwamnati ta kara bullo da wasu hanyoyi na magance cin hanci da rashawa tare da bin tsarin da zai yi daidai da manufofin ‘yan kasa.
Musa ya ce hakkin tabbatar tsaro al’amari ne da ya shafi kowa da kowa, ba kawai hakki ne na gwamnati kadai da masu sanye da kayan sarki ba.
Ya ce dole sai ’yan kasa sun hada hannu da mahukunta tare da bai wa jami’an tsaro ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaro musamman a Arewacin kasar nan.