Yawan hanzari na jawo asara
Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Yawan hanzari na jawo asara’. Labarin na kunshe ne da yadda A’isha ta yi asarar karenta sakamakon hanzari. A sha karatu lafiya. Taku: Gwaggo Amina Abdullahi Yawan hanzari na jawo asara A wani lokaci da ya shude an […]
Barka da warhaka Manyan Gobe
Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Yawan hanzari na jawo asara’. Labarin na kunshe ne da yadda A’isha ta yi asarar karenta sakamakon hanzari.
A sha karatu lafiya.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi
Yawan hanzari na jawo asara
A wani lokaci da ya shude an wata mata da ake kira A’isha da ke zama a kauyen Koko. Tana da ‘ya daya da kare. Karen nata yana taimaka mata wajen tsaron jinjirarta ‘yar wata 2.
Wata rana ta shirya za ta kasuwa sai tasa karen ya kula mata da yarta kafin ta dawo.
Jim kadan bayan ta tafi sai wani maciji ya zo kusa da gadon jinjirar yana kokarin ya sare ta. Da ganin hakan, sai karen ya je da gudu ya kashe macijin. Sai ya koma bakin kofar dakin domin ya ci gaba da tsaron jinjirar.
A’isha na dawowa sai ta sami kare bakinsa duk jini. Ganin hakan sai ya sa ta yi zaton ya kashe mata ‘yarta ne, sai ta dauko wuka ta kashe shi. Isarta cikin daki, sai ta ga ‘yarta a kwance tana wasa kuma ga gawar maciji a gefe.
Nan ta gane cewa ashe karen ya taimaka mata ne, sai ta fasa kuka.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin. Da a ce A’isha ta yi bincike ba ta kuma yi saurin yanke hukunci ba da hakan bai faru ba.