‘Yawan haraji ke nakasa kasuwanci a Najeriya’

Aminiya ta tattauna da Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da masu masana’antu da aikin gona (KADCCIMA), na Jihar Kaduna, Dakta Abdul Alimi Bello, inda ya bukaci gwamnati ta inganta harkar kasuwanci. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Yaushe ne za a fara kasuwar baje-koli ta kasa ta wannan shekara?Alimi Bello: A watan gobe za a gudanar […]

‘Yawan haraji ke nakasa kasuwanci a Najeriya’

Aminiya ta tattauna da Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da masu masana’antu da aikin gona (KADCCIMA), na Jihar Kaduna, Dakta Abdul Alimi Bello, inda ya bukaci gwamnati ta inganta harkar kasuwanci. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Yaushe ne za a fara kasuwar baje-koli ta kasa ta wannan shekara?
Alimi Bello: A watan gobe za a gudanar a dandalin baje-koli na dindindin da ke Rigachikun kan titin Zariya a Kaduna.
Aminiya: Mene ne ra’ayinka dangane da yawan haraji ga masu kamfanoni?
Bello Alimi: Abin yana da ban haushi matuka. Dalili kuwa shi ne, za mu biya gwamnatin tarayya haraji, mu biya ta jiha, sannan mu biya karamar hukuma, mu kuma biya kudin kayan alfarma da na irin bangaren da ya shafe mu ko na kere-kere da sauransu. Bayan nan za mu biya kudin wuta, da na ruwa, da sayen dizel da biyan ma’aikata da sauransu. Ana biyan kashi 5 cikin 100 yanzu ga kayam alfarma, abubuwan sun yi tsanani sai ga shi za a kara haraji ya koma kashi 10 cikin 100, ina za a je da wannan rashin hangen nesa? Daga ina za a samo kudin da za a biya? Hakan zai mayar da kasa baya ne kawai, domin zai nakasa kasuwanci.
Aminiya: Yaya kake ganin wannan sabon karin ke nan?
Bello Alimi: Nan ba da dadewa ba ’yan kwadago za su so a kara musu kudin albashi. Wani lokacin idan na yi la’akari da yadda hukumar tara kudaden shiga ta kasa ke aiki, gaskiya akwai gyara.
Aminiya: Kamar shekara nawa kuka kwashe kuna shirya baje-koli?
Bello Alimi: A wannan gamayya ta ’yan kasuwa, mun yi kusan shekara 10 ke nan. Mun samu nasarori, mun kuma fuskanci matsaloli. A yanzu muna la’akari da wuraren da suka kamata mu kara himma don mu ci gaba da samun nasara.
Aminiya: Ana samun sauye-sauye dangane da yanayin tsaro?
Bello Alimi: Eh, ana samu saboda tsaro. Tun da muka bar Dandalin Murtala da ke Kaduna zuwa Rigachikun saboda yana bayan gari, muna kara lura da yanayin tsaro matuka da gaske. Don da a ce muna Dandalin Murtala har yanzu, to ai da tsaron ya fi haka matuka.
Aminiya: Yaya batun shirin zirga-zirga?
Bello Alimi: A lokacin da muke da ’yan uniyon a kasuwarmu, masu motocin haya ba su samun matsala wajen mayar da masu cin kasuwa cikin gari.
Aminiya: Akwai sabbin sauye–sauye don jin dadin jama’a?
Bello Alimi: Mun fito da hanyar samun kudin shiga, inda muke karbar don kudi a wurin jama’a don su kalli namun daji a filin kasuwar duniya. Musamman ’yan makaranta da ke jin sunayen dabbobi ba tare da sun taba ganin su ba. Wannan shirin ya samu karbuwa matuka.
Aminiya: Darajar Naira na ci gaba da faduwa, mece ce illar hakan ga kasuwanci?
Bello Alimi: Dillancin kudaden waje na Babban Bankin Najeriya (CBN) na neman gyara. Aikin CBN ne inganta darajar kudin Najeriya. Kuma faduwar darajar Naira laifin CBN ne. Kwanaki mun gana da ’yan jarida kan yadda ake yin cinikin shunku. ’Yan kasuwa na fama da rashin samun rance daga bankuna, mece ce mafita? Ya kamata a ce Bankin Aikin Gona da ke da hedkwata a Kaduna ya kara yin shiri mai sauki. Amma Bankin Masana’antu ba su yi gyara ba dangane da yadda talaka zai ci moriya aikinsa. CBN ya ce ta hannun Bankin Masana’antu ne za a samu jarin inganta masana’antu, amma wannan Gwamna Bankin Najeriya Godwin Omefiele ya dakatar da hakan. Faduwar darajar Naira babu kyau. Amurkawa na son a kullum su ci gaba da danne kasashe ne kawai, don me za mu rage darajar kudinmu? Idan mutum ya sayo motar Naira miliyan daya sai to koma Naira miliyan daya da dubu 500, to yaya za a sayar da ita?
Faduwa darajar Naira matsala ce. Ba ka da gida, ba ka da darajar kudi, sannan kudin ruwa ya harba sama, kasuwancin ya tsaya, ba za ka iya samun bashi mai sauki ba, don bashin na tare da sarkakiya. Abin da ban takaici matuka.
Aminiya: Amma gwamnati na ci gaba da cewa tattalin arziki ya bunkasa?
Bello Alimi: A takarda ya bunkasa, amma a zahiri koma baya aka samu. A yanzu a kasar Sin an fara “Phamton Fair”, wato baje-kolin kaya a ragowar farashi sau biyu a shekara. A da mutane da yawa suna zuwa don sayo kaya a watan Afrilu, amma saboda faduwar Naira musamman ma idan ka yi kiyasin kudin da za ka kashe, misali, idan kana da Dala dubu 10. In ka cire kudin jirgi da sauransu, nawa ribarka? Amma duk wanda ya yi lissafi ya ga ba zai ci riba ba, to sai ya fasa ba.