Yawan ɗanyen mai da Najeriya ke haƙowa ya ragu
A kullum ana rasa ganga 160,000 na ɗanyen mai a tsawon watanni uku da suka gabata a Najeriya.
Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta sanar cewar yawan ɗanyen mai da ƙasar ke haƙowa a kullum ya ragu da gangan 160,000.
NBS ta bayyana cewa adadin ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa domin fitarwa kasuwannin duniya ya ragu zuwa ganga miliyan 1.41 daga ganga miliyan 1.57.
Ta bayyana cewa an samu raguwar haƙo danyen man ne a tsakanin watan Afrilu zuwa watan Yuni na shekarar 2024 muke ciki.
Sai dai ta bayyana cewa duk da haka, yawan kayan da ake samarwa a Najeriya ya karu da kashi 3.19 a cikin 100.