Yawan manta katin shaida ya sa an zana masa hoton katin a jiki

Wani matashi daga kasar Bietnam da ke tuhumarsa da yawan mance katin shaidarsa na dan kasa idan ya je mashaya da abokansa, hakan ya sa an yi masa zanen tattoo na katin a hannunsa. An yi ta yada hotunan da ke nuna alamar shaidar katin dan kasa da aka zana a hannunsa, musamman a shafukan […]

Yawan manta katin shaida ya sa an zana masa hoton katin a jiki

Yawan manta katin shaida

Wani matashi daga kasar Bietnam da ke tuhumarsa da yawan mance katin shaidarsa na dan kasa idan ya je mashaya da abokansa, hakan ya sa an yi masa zanen tattoo na katin a hannunsa.

An yi ta yada hotunan da ke nuna alamar shaidar katin dan kasa da aka zana a hannunsa, musamman a shafukan sadarwar zamani na kasar Bietnam. Wani da ya wallafa tuhumar ya ce, daya daga cikin abokansa idan yana cikin wani yanayi yana yawan batar da katin shaidarsa na zama dan kasar idan ya je kulob din shakatawa. Sakamakon yawan batar da katin shaidar da yake yi ya sa, kuma shi bai yarda ya tsufa da shan giya ba, saboda yawan batar da katin shaidar da yake a mashayar wanda a tunaninsa za a iya dakatar da shi daga zuwa kulob din. Sai ya yanke shawarar a zana masa masa hoton katin shaidar a hannunsa irin zanen tattoo.

Kafar labarai ta Tinmoi, ta ce, “Akwai wani abokin mashayin giyar da yake zaune a birnin Ho Chi Minh da yake sha’awar fita mashaya da abokansa, amma duk lokacin da ya zo shiga harabar mashayar sai ya ki nuna katin shaidarsa wanda hakan zai sa a hana shi shiga. Mashayin sai ya yanke shawar shiga shagon zanen tattoo don zana masa hoton katin shaidar a jikinsa saboda gudun hana shi shiga mashayar,” kamar yadda kafar ta sanar.

Wadansu masu bibiyar shafuffukan sadarwa sun yi ta yada hotunan a shafukan sada zumunta, wanda hakan ya dau hankalin jama’a da dama, saboda sukan hoton da ake yi cewa, yana daya daga cikin munanan zanen tattoo da aka taba yi.

Wani da yake mu’amala da shafin sada zumuntar ya ce, da farko da na ga ana yada hoton zanen tattoo na yi tunanin na bogi ne, amma daga bisani, na gano wanda ya yi zanen, saboda ya dade yana irin wannan zane, wannan ne karon farko da wani ya ce, ya zana masa katin shaida a jikinsa.

Wanda ya yi zanen mai suna Nguyen Ban Thien Dai, ya yi mamakin bukatar wanda ya zo ya ce, a yi masa zanen, da farko ya ba shi shawara amma bai amince ba sai yanke shawarar yi masa abin da yake so.

A cewar Nguyen Ban, zanen ya dauke ni kusan sa’a daya ina yi kafin in kammala.

Nguyen Ban, ya ce wannan zanen ba zai zama kamar shaidar da za a bar wadansu su shiga kulob din shakatarwar ba, saboda wannan zane ne kawai.

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno

Lokacin Soke Tallafin Mai A Najeriya Ya Yi —Dangote

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta sha daƙile yunƙurin hargitsa ƙasar

Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m