Yawan masu dauke da coronavirus ya karu da 245
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan sun nuna cewa an samu karuwar wadanda aka tabattar sun kamu da mutum 245. Da hakan ne dai jimillar wadanda suka kamu a kasar baki daya ya tashi 2,808, kamar yadda hukumar ta ce: “Zuwa karfe 11.45 na daren 3 ga watan […]
Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan sun nuna cewa an samu karuwar wadanda aka tabattar sun kamu da mutum 245.
Da hakan ne dai jimillar wadanda suka kamu a kasar baki daya ya tashi 2,808, kamar yadda hukumar ta ce:
“Zuwa karfe 11.45 na daren 3 ga watan Mayu, mutum 2,808 aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya; 417 daga cikinsu an sallame su bayan sun warke yayin da 93 suka riga mu gidan gaskiya”.
Jihar Legas ce dai ke kan gaba da yawan sabbin kamun, da mutum 76, sai Katsina mai biye mata da mutum 37.
An kuma samu sabbin kamu 32 a Jigawa, 23 a Kano, 19 a Yankin Babban Birnin Tarayya, 18 a Borno, da kuma 10 a Edo.
Sauran jihohin su ne Bauchi mai mutum tara, da Adamawa mai shida, sannan Oyo da Ogun masu mutum biyar ko wacce.
Su kuwa jihohin Ekiti da Osun da Binuwai da Neja da Zamfara suna da mutum guda-guda.
Wuraren da ke kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu su ne Legas, da Kano, da Yankin Babban Birnin Tarayya da mutum 1,183, da 365, da kuma 297 daki-daki.