Yawan mutanen Najeriya ya kai miliyan 216 a bana —MDD

Yawan mutane a Najeriya shi ne kashi 2.7 na al’ummar duniya.

Yawan mutanen Najeriya ya kai miliyan 216 a bana —MDD

Najeriya

Yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 216 a shekarar 2022, wanda hakan ya kai kashi 2.7 na al’ummar duniya.

Sashen Tattalin Arziki da Zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana alkaluman cikin wani rahoto da ya fitar.

Hakan na nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashe takwas da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Masar, Habasha, Indiya, Pakistan, Philipines da Tanzaniya da ke ba da gudunmawa wajen saurin karuwar yawan mutane a duniya.

A duk lokacin da mutum ya shiga cibiyoyin lafiya a matakin farko ko asibitocin haihuwa, zai ga dafifin mata masu juna biyu a Najeriya ko kuma wadanda su ka kawo jariran su rigakafi.

Dokta Adama Ibrahim Jibril da ke aiki a asibitin mata da yara a Jihar Kano, ta ce matan na fahimtar muhimmancin bayanan tazarar haihuwa da kula da yara ko da kuwa ba dukan su ke samun nasarar aiwatar da shawarwarin da aka ba su ba.

Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Najeriya NPC da ke shirin kidaya a Afrilun badi, ta tabbatar da ingancin rahoton na Majalisar Dinkin Duniya.

Dokta Ahmad Sagir na Asibitin Koyarwa da ke Gwagwalada, ya ce likitoci da jami’an kula da lafiya na kokarin wayar da kan jama’a wajen muhimmancin tazarar haihuwa don taimakon lafiyar jarirai da uwayen su.

Kungiyoyin kula da hakkokin kananan yara na kokawa kan yadda mutane kan haifi yara ba tare da kula da su ba ta hanyar barin su suna gararamba kan tituna.

Sa’idu Sambo Kaftan da ke da kungiyar raya ilimin yara a Arewa, ya ce sukan samu yara da yawa da iyayen su suka fita sha’anin su musamman don talauci ko halin ko in kula.

Alkaluma sun nuna zuwa shekara ta 2050, adadin mutanen duniya zai karu daga mutum biliyan 8 zuwa biliyan 9.75.