Yawan ’yan gudun hijirar Ambazoniya a Najeriya ya ninka 5 cikin wata uku
’Yan gudun hijirar kasar Kamaru da ke fafutikar kafa kasar Ambazoniya da suka kwararo zuwa wasu kananan hukumomin Jihar Kuros Riba ya ninka sau biyar daga watan Oktoba zuwa Disamban bara. Yawansu ’yan gudun hijira ya karu daga mutum dubu 5, zuwa dubu 25 cikin wata uku. […]

’Yan gudun hijirar kasar Kamaru da ke fafutikar kafa kasar Ambazoniya da suka kwararo zuwa wasu kananan hukumomin Jihar Kuros Riba ya ninka sau biyar daga watan Oktoba zuwa Disamban bara. Yawansu ’yan gudun hijira ya karu daga mutum dubu 5, zuwa dubu 25 cikin wata uku. Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (SEMA) ta Jihar Kuros Riba, Mista John Inaku ne ya shaida wa wakilinmu haka.
’Yan gudun hijirar da ake kiransu da ’yan awaren Kamaru, suna zaune a kananan hukumomin Akamkpa da Akpabuyo da Birnin Kalaba da Kalaba ta Kudu da Ikom da Boki da Obudu da kuma Etung, wadda taf i kusa da iyakar kasar Kamaru.
’Yan gudun hijirar, kamar yadda wakilinmu ya binciko, suna zaune ne a gidajen ’yan uwa da abokan arziki, ba a sansani daya ba. Sai kuma ga jandarmomin Kamaru sun rika kawo musu hari a inda suke makale, lamarin da wadansu jama’a ke ganin idan ba a yi hattara ba, zai iya zama yaki tsakanin kasashen biyu.
Tun da farko dai Jamhuriyyar Kamaru ta zargi Najeriya cewa tana horar da ’yan awaren Ambazoniya a boye, yayin da wadansu kuma ke zargin mika daya daga cikin shugabannin kungiyar da Najeriya ta yi ga Kamaru ya haifar da cece-ku-ce tsakanin kasashen biyu.
Aminiya ta ziyarci karamar Hukumar Etung, inda ta zanta da wadansu daga cikin ’yan gudun hijirar da ke zaune a garin Abokim Obi da Agbokim Waterfalls. Regina Agbor wadda ta tsallako daga Nsasarati, ta kasar Kamaru ta bayyana yadda aka yi ta tsira daga cin zarafin jandarmomin Kamaru, inda ta ce a halin da ake ciki har yanzu ba ta san inda ’yarta daya take ba. “Muna zaune lami lafiya sai muka fara jin harbe-harbe a cikin dare, ni kuma ba na gida, ba ni kadai ba ce wurin mijina, ina da kishiya. Wayewar gari ke da wuya sai jandarmomi suka rika korarmu, suna cewa kowa ya fita, ni kuma da na ji haka da ma ’ya’yana suna daki na kulle su. Na tunkari gida sai jandarmomi suka bi ni suna tambayata inda za ni, wani kuma yana cakumo ni, na ce ’ya’yana zan dauko a gida. Koma me za ku yi mini sai na je. Duk da na tsorata ko za su bi ni ciki su yi mini fyade, haka na fito na kwaso ragowar yara uku, babbar ce ban san inda ta yi ba. Nan inda ka same mu ’yan uwa da abokan arziki ne da muka hada harshe daya suka ba mu mafaka,” inji ta.
Shi kuwa Eniebong Jerome, makaho mai kimanin shekara 70, ya ce lokacin da abin ya faru, ya ji harbe-harben bindiga amma “Ni ba gani nake yi ba, na ji mutane na ta gudu suna cewa kowa ya yi ta kansa. Ni da ba ido ina za ni? karshe su jandarmomin ne suka fitar da ni, suka kawo kan hanya suka ajiye. Daga bisani kuma iyalaina suka gano inda nake, suka kawo ni wajen surukina, wanda shi ne yake kula da mu. Mu wajen 28 ne yake kula da mu, yake taimaka mana. Ni rokona ga gwamnatin Kamaru shi ne, a sasanta mu koma gida, nan zaman da muke munatakure ne. Abinci ma ba don Allah Ya sa suna ba mu ba, da ba mu san yadda za mu kare ba,” inji shi.
Ita kuwa Nguma Therasi, wata budurwa da Aminiya ta tarar tana sassara asuwaki. Da ta tambaye ta ko yaya rayuwa ta kasance musu kuma ta yaya take tallafa wa kanta, ganin cewa sun baro gida sai ta ce: “Zaune nake ba na sana’ar komai, wannan ma maganin zama haka ne nake taimaka wa mai aikin asuwaki. Da haka nake samun abin da zan ci.”
Aminiya ta zanta da Daraktan Hukumar SEMA ta Jihar Kuros Riba, Mista John Inaku kan abin da suke yi wajen kula da ’yan gudun hijirar, inda ya ce, “Duk matsalolin da suke kokawa a kai na rashin abinci ko magunguna, lokacin da suka zo, dan abin da ake da shi a gwamnatance shi aka yi amfani da shi wajen ba su abinci da makwanci. Lokacin yawansu mutum dubu 5 ne kafin karshen shekara suka kai mutum dubu 25. Zancen nan da muke yi da kai yanzu haka ana da sama da mutum dubu 33. ’Yan gudun hijirar ba su a cikin kasafin kudin gwamnatin Kuros Riba kuma Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ma ta yi bakin kokari, har yanzu yawansu a kullum karuwa yake yi.”
Da aka tambaye shi kan harin da jandarmomi suka kawo wa ’yan gudun hijirar, Daraktan ya ce masu bi ta ruwa ne suka gamu da haka, yanzu sun gwammace su yanki daji su shigo Najeriya.