Yawon-darar Baban-gada-gada
Gwamnan Jihar Ni-na-ja, mai burga da baragada ya fara yawon-dara a rikicinsu na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, inda yake nuni da cewa ya balle daga bangaren Kawun Bararrajewa zuwa gidan Banga-Banga Tukururu. Kuma da safiya sakaliya, sai a daukacin jaridun kasar Haurobiya, wadanda suka hada da Balon-faranti da Faffale dalili da ’Yar […]
Gwamnan Jihar Ni-na-ja, mai burga da baragada ya fara yawon-dara a rikicinsu na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, inda yake nuni da cewa ya balle daga bangaren Kawun Bararrajewa zuwa gidan Banga-Banga Tukururu. Kuma da safiya sakaliya, sai a daukacin jaridun kasar Haurobiya, wadanda suka hada da Balon-faranti da Faffale dalili da ’Yar Yau da Ladar-shafi sun fito da batun mai burga da baragada, inda ya bayyana cewa batun komawarsa gidan Tukururu zuki-ta-malle ce. To wanne ne, ba wanne ne ba?
’Yan makaranta kada batutuwan Gwamnan Ni-na-ja su karkatar da hankulanku, domin shi mutum ne da ya kware wajen tafka ta’asa da tabargaza, ga kwakyariya iri-iri. Idan ahr ba ku ari faden Malam Mantau ba, za ku iya fasko cewa a farfajiyarmu ta Dodorido mun tabba bijiro da batutuwa kan yadda Gwamna Gwaramgwam ya tabbatar wa Bahagon Babban mutum mai rawani cewa shi ba ya shaye-shaye da romo. “Billahilazi la’ilaha illahuwa fura ma idan ta cika tsami ba ma sha, amma sai su ce jibi namujiyarsa kururu,” a cewarsa, ranar bikini idin shekara ta dubu karamin lauje da madambaci.
Daga cikin hujjojin da ka ruwaito Baban-gada-gada ya bayyana na tsallen badake daga wannan sheka zuwa waccan sheka, sun hada da cewa shi fa mai digirgire ne da digirin ilimi har kofar hanci, don haka bai kamata ya biye wa wadanda ba su da cikakkiyar shaidar kwarewa a harkokin watsattsake da buda wagagen littattafai. Sannan ya kara da cewa, Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa, ya aiko ana ta zawarcinsa, don ya zo su ci gaba da gudu a cikin loko.
A matsayina na babban direban alli a wannan makaranta, na fasko cewa Baban-gada-gada yana son ya nuna wa Gwamna Mai Kwarankwatsin-tsiya na birnin Dabo da Mai sunan Sulalla na Jihar Jijjiga-ciyawa, cewa shi gwanin wasan kwado da dara ne, don haka yake bukatar buka ta-mola da kwakwalen al’umma. Kowa ya san cewa mafi yawan jiga-jigan ‘yan siyasar Haurobiya wasan Samson-siya-siya suke yi da kwanyar al’umma, shaida a kan haka, Shugaban Jam’iyya Mai dan boto da sanda Jirge, Banga-Banga Tukururu, ya taba bayyana wa duniya cewa shi ne Mesi, wato yana nufin “wanda ya ci kambin gurasa gami da masa ga wasa-wasa a zuba a kwanon tasa, ’yan kasa su yi kwasa ba wani wasa.’ Yau dai kowa ya ga yadda Mesi ya zama masa. Shi ma Baban-gada-gada karshen yawon dararsa yana gab da karatowa.
Haurobiyawa kada ku damu da mai yawon dara, domin ko Baban-gada-gada ya koma gidan Tukururu ko ya Bararraje, babu abin da ya dada mu da kasa, tunda mun fasko cewa al’umma ta kosa da ganin karshen mulkin mulaka’u na mai dan boto da sanda jirge. karkashin jagorancin wannan jam’iyya Haurobiya ta afka cikin rikicin Haramta Bobo da kwambon bokoko; aka cefanar da daukacin kadarorin gwamnati, bisa tsarin gwanjo, dakan daka, shikar daka da tankaden baking ado. An lalata kowace farfajiya ta koyon watsattsake da buda wagagen littattafai, tun daga matakin Fura-mai-kyau zuwa jam’in jama’ar jami’o’in kasar Haurobiya, har ta kai ga an kasa yin bikon jami’an Asusun ilimi da suka yi yaji.
Babbar nasarar da mulkin mulka’un mai dan boto ya samu a kasar Haurobiya, shi ne share wurin zaman dirhsan ga kwashi-kwaraf, inda ta kai ga an kori Gogarma Rubdigau daga mukaminsa, aka nada Mai fari da idanu cikin bakar kwalba, ia kuwa ta yi ta rausayar ’yan matancinta; yau kuwa ga Loma-a-murde ya zama Muzurun Lami.
Duk wand ake baje na-mujiyarsa a gaban akwatin amgana mai hoto ko mara hoto, tare da daukacin masu falle shafukan jaridu da mujallu da makalu, sun fasko yadda Santala kwaiduwa ta cirri tutar kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Wannan mata kamar yadda muka bijiro da batunta a makon da ya arce, ta yi wa manyan Haurobiya fintikanu wajen raruke lalitar kasar nan. Don haka ma a yau, sai dai Araruma da ’Yar’didi su rika take mata baya. Hasalima ta yi wa Farfesun Borin-shorido gudun yada kanen wani, wajen yi wa tsuntsayen Haurobiya kakkabar ’ya’yan kadanya.
Haurobiyawa, ya kamata ku fasko cewa sai an kula kashi yake doyi, don haka ku yi shakulantun bangaro da Baban-gada-gada, ya yi ta tsallen badakensa. A can Jihar Ni-na-ja, har talakawa su yi masa jifar shaidan. Masu yawon-dara da kwado, don neman hanyar wawushe lalitar kasa, ya kamata ku san cewa an fasko suddabarunku. Sai ku yi hanzarin sake salo.