’Ya’ya da iyayen da suka yi digiri a jami’a guda a kasashen duniya
Peng dianghu, wani uba mai shekara 51 da ke aiki a Lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin ya samu shiga jami’a guda da ’yarsa ‘yar shekara 19, kuma ya samu yabo daga dimbin al’ummar da ke hada-hada a shafukan intanet, bisa la’akari da kwazonsa wajen neman ilimi. “Ina sha’awar samun wani ilimi daban, don […]
Peng dianghu, wani uba mai shekara 51 da ke aiki a Lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin ya samu shiga jami’a guda da ’yarsa ‘yar shekara 19, kuma ya samu yabo daga dimbin al’ummar da ke hada-hada a shafukan intanet, bisa la’akari da kwazonsa wajen neman ilimi.
“Ina sha’awar samun wani ilimi daban, don haka nike matukar jin takaicin rashin samun damar yin karatun jami’a tun farko,” kamar yadda ka jiwo daga bnakin Peng.
An haifi Peng a shekarar 1966, ya daina zuwa babbar makarantar sakandare ta birnin Shahe da ke diatai, a Lardin Hebei da ke Arewacin kasar Sin., lokacin yana da shekara 17 saboda iyayensa na fama da talauci a lokacin, kamar yadda rahoton jaridar Zhengzhou mai fitowa kowane yammaci ta bayyana.
Bayan ya daina makaranta sai ya yi ayyuka da dama a matsayin ma’aikacin da ya yi kaura (daga wannan wuri zuwa wancan), inda ya yi aiki a masana’antu, sannan ya sayar da gayayyaki da kayan marmari.
Peng ya kara kwazon aiki bayan da ya yi aure, saboda akwai bukatar daukar dawainiyar iyalansa, da biyan kudin makarantar ’ya’yansa uku.
“Kuma aikin karfi kawai zan iya yi saboda ban yi karatun zamani ba,” a cewar Peng, inda ya yi nuni da cewa shekaru 30 da suka wuce mafarkinsa kawai ya halarci jami’a. A bara ’ya’yansa biyu suka kammala karatun jami’a, sannan karamar cikinsu ta rubuta jarrabawar shiga jami’ar.
Da naga daukar dawainiyar iyali ta ragu, sai na fara aro littattafai daga manyan makarantu, inda daga bisani nima na rubuta jarrabawar shiga jami’ar a bana.
A Satumbar bana ya samu nasarar shiga jami’ar Hebei ta Injiniyancin kula da Muhalli.
“Ina mai alfahari da mahaifina don ya zamo abin koyina,” a cewar ’yarsa Peng Songhua, wadda ta shiga jami’a tare da shi.
Wannan uba da ’yarsa tuni suka shahara a jami’ar, sannan sun samu dimbin yabo daga masu mu’amala da kafar sadarwar intanet.
A kasashen duniya an samu irin wadannan al’amura, wato inda uba da ’ya suka kamala karatun jami’a tare, wato kamar a Birtaniya, inda Cloe Jackson ’yar shekara 22 ta kammala jami’ar Gordon (RGU) tare da mahaifinta Billy Jackson. Sannan a kasar Saudiyya ma Wani uba mai shekara 47 Abdulla Awad Al-Sulaimi da dansa Khalid sun kasance a jein mutum 32 da suka kammala digirinsu a fannin darussan addinin Musulunci daga Jami’ar Taiba da ke Medina.