’Ya’ya za su iya amfani da sunan mahaifiya a takardun hukuma a Indiya

’Ya’ya za su iya amfani da sunan mahaifiyarsu a takardun hukuma, kuma mata na da zabin amfani da sunan mahaifin su ko na mijin su,’ kamar yadda dokar sashen walwala da kyauta jin dadin Mata da knanan yara na Jihar Maharashtra a Indiya ya tanada.“’Ya’ya na da zabin amfani da sunan mahaifiyar su ko mahaifin […]

’Ya’ya za su iya amfani da sunan mahaifiya a takardun hukuma a Indiya
’Ya’ya za su iya amfani da sunan mahaifiya a takardun hukuma a Indiya

’Ya’ya za su iya amfani da sunan mahaifiyarsu a takardun hukuma, kuma mata na da zabin amfani da sunan mahaifin su ko na mijin su,’ kamar yadda dokar sashen walwala da kyauta jin dadin Mata da knanan yara na Jihar Maharashtra a Indiya ya tanada.
“’Ya’ya na da zabin amfani da sunan mahaifiyar su ko mahaifin su,” kamar yadda yake dauke a Dokar Gwamnati da Sashen Walwala da jin dadin mata da yara ya fitar a Jihar Maharashtra ta kasar Indiya. Wannan kuywa yana cikin wani kuduri da aka yanke matsaya a kan sa tun a shekarar 2014, cikin watan Maris.
Duk macen da ta samu matsala wajen aiwatar da zabinta, za ta iya gabatar da korafinta ga jami’in tattara bayanai na gunduma. Su kuwa kananan yara suna da zabin rubuta sunayen iyayensu (uwa da uba) ko kuma su zabi daya daga cikin su, kamar yadda ya ke kunshe a cikin kundin.