Yaya za ta kaya a zaben shugabancin Majalisar Tarayya ta 10?

Za mu tabbatar da ba a yi wannan abin da uwar jam’iyyar APC ta ce ba.

Yaya za ta kaya a zaben shugabancin Majalisar Tarayya ta 10?

Majalisar Tarayya

Kura na kara tirnikewa a kan batun zaben shugabancin Majalisar Dokokin Tarayya ta 10 wanda ake sa ran kaddamar da ita yau Talata, inda za ta zabi shugabanin ta wadanda za su gudanar da aiki na tsawon shekaru hudu.

Amma duk da kurewar lokaci, akwai takaddama ta cikin gida a jam’iyyar APC mai mulki, da ka iya jawo mata rasa kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, duk da cewa uwar jam’iyya ta fito da wadanda ta ke so a zaba a matsayin shugabani a majalisun biyu wato da majalisar wakilai da ta dattawa.

Takkadamar ta yi kamari tsakanin kungiyoyin jam’iyyar APC mai mulki da wadanda suka fito takarar neman kujerar shugaban Majalisar Dattawa, da suka hada da APC Integrity Group da suke goyon bayan Osita Izunaso, sai APC Amalgamated da ke goyon bayan Abdulaziz Yari.

Ita kuwa uwar Jamiyyar APC tana goyon bayan Godswill Akpabio da mataimakin sa Barau Jibrin. Amma Majalisar tana kara dagewa domin nema wa kanta ’yanci a zaben wadanda za su zama shugabanni kamar yadda Sanata Suleiman Kawu Sumaila ya yi bayani cewa wannan dambarwa ce da aka saba yi amma na wannan karon ta zo da bakon al’amari.

Kawu ya ce jam’iyya mai mulki ta fito da sunayen ‘yan takara, amma da shi da ’yan uwansa wadanda majalisa ta ke jinin su, za su tabbatar da ba a yi wannan abin da uwar jam’iyyar APC ta ce ba, domin kar tarihi ya maimaita kan sa nan gaba. Kawu ya ce “bin irin wannan umurni, danniya ce irin ta soja.”

A kyale ’yan majalisa su zabi ra’ayinsu —Dattawan Arewa

A na shi nazarin kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Hakeem Baba Ahmed ya fito ya goyi bayan Kawu Sumaila ne, inda ya ce sam uwar jam’iyyar APC ba ta kyauta ba da ta yi wa majalisa katsalandan.

Hakeem ya ce ko wane bangare na gudanarwa yana cin gashin kansa ne, saboda haka ’yan majalisa suna da ‘yancin zaben duk wanda suke so ba tare da bin umurnin kowa ba.

Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF ta kuma bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya girmama doka ya kyale ’yan Majalisar Dokokin Tarayya su zabi wadanda suke so su shugabance su.

A cewar kungiyar, bangaren majalisa waje ne mai zaman kansa, don haka ya zama wajibi bangaren zartarwa ya guji yi masa shisshigi wajen zaben shugabancinsa.

Dokta Hakeem Baba-Ahmed wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna ranar Litinin ya kuma yi martani ga kalaman Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima kan batun.

Aminiya ta rawaito yadda Shettiman ya tara Sanatoci yana cewa komai lalacewar Kirita dan Kudu ya fi cancanta ya jagoranci Majalisar Dattawa a kan Musulmi dan Arewa, komai cancantarsa, kodayake daga bisani ya ce canza masa kalaman aka yi.

To sai dai Dokta Hakeem ya soki kalaman na Shettima, inda ya ce abin takaici ne, kasancewarsa Musulmin da ake girmamawa, kuma dan siyasa.

Ya ce a lokuta da dama, kungiyar ta sha rokar Tinubu da ya kyale doka ta yi halinta kyale ’yan majalisar su zabi wanda suke so ya jagorance su, ba wai a kakaba musu wadanda ba sa so ba.

“Kungiyar Dattawan Arewa a lokuta daban-daban, ta shawarci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta girmama ra’ayoyin ’yan majalisar don tabbatar da tsari da yin abu a tsari,” in ji Dokta Hakeem.

ACF ta yi Allah-wadai da harin Sakkwato, ta nemi a yi bincike

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9