’Ya’yan APC a Kalaba sun yi shagulgulan murnar lashe zaben Shugaban Kasa

Magoya bayan Jam’iyyar APC da ke Nasarawa-Bakoko da kuma wadanda suke a Unguwar Hausawa, Layin Bagobiri a Kalaba, sun gudanar da shagulgulan samun nasarar Shugaba Buhari a zaben Shugaban Kasa da aka kammala ranar Asabar da ta gabata. Da yake yi wa Aminiya karin haske Kakakin Jamiyyar APC a Mazaba ta Daya a Karamar Hukumar […]

’Ya’yan APC a Kalaba sun yi shagulgulan murnar lashe zaben Shugaban Kasa

Magoya bayan Jam’iyyar APC da ke Nasarawa-Bakoko da kuma wadanda suke a Unguwar Hausawa, Layin Bagobiri a Kalaba, sun gudanar da shagulgulan samun nasarar Shugaba Buhari a zaben Shugaban Kasa da aka kammala ranar Asabar da ta gabata. Da yake yi wa Aminiya karin haske Kakakin Jamiyyar APC a Mazaba ta Daya a Karamar Hukumar Kalaba, Bala Yakubu ya bayyana dalilan da suka sanya su yin shagulgulan “Saboda murnar  Baba Buhari ya samu  nasarar lashe zabe karo na biyu shi ya sa muke wannan murna domin mu nuna goyon bayyanmu dari bisa dari da fatan Allah Ya taimake shi Ya taya shi riko,” inji shi.

Akasarin wadanda aka zanta da su a wuraren shagulgula na Nasarawa Bakoko da Unguwar Hausawan sun bayyana matukar farin cikinsu tare da fatan a ci gaba da ba Shugaban Kasa goyon baya da ta ya shi addu’ar Allah Ya ba shi ikon ci gaba da aikin da ya fara shekara a hudunsa na farko na tabbatar da tsaro da farfado da noma da tattalin arziki da kuma hada kan jama’a.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno