’Ya’yan Michael Jackson za su rika samun alawus din Naira bilyan biyu da rabi duk shekara
A sakamakon makudan kadarori da dukiyar da marigayi Michael Jackson ya bari kuma da yadda take ta kara habaka, a yanzu ’ya’yansa guda uku za su rika samun alawus na Naira biliyan biyu da rabi a kowace shekara (Dala miliyan takwas).Kamar yadda labari ya bayyana, yaran za su rika kashe wadannan makudan kudi ne wajen […]

A sakamakon makudan kadarori da dukiyar da marigayi Michael Jackson ya bari kuma da yadda take ta kara habaka, a yanzu ’ya’yansa guda uku za su rika samun alawus na Naira biliyan biyu da rabi a kowace shekara (Dala miliyan takwas).
Kamar yadda labari ya bayyana, yaran za su rika kashe wadannan makudan kudi ne wajen tafiyar da rayuwarsu, wadda ta hada da biyan kudaden makaranta, yawace-yawacen hutu domin shakatawa da sauransu.
Shi dai Michael ya mutu ne a 2009 a sakamakon zargin da aka yi wa likitansa na cewa ya yi masa aringizon maganin rage radadi. A daidai lokacin, an yi zargin cewa bashi ya yi masa katutu, domin an ruwaito cewa ana bin shi bashin Naira biliyan 128 (kimanin Dala miliyan 500). Bayan mutuwarsa ne sai kadarorinsa suka rika yin daraja kuma suka rika samar da makudan kudade ga magadansa. Musamman an samu rahoton cewa faya-fayen wakokinsa sun rika yin kasuwa, inda suka rika kawo wa magadansa kudi masu yawa kamar ruwa. Akalla an sayar da kwafi miliyan hamsin na faya-fayen wakokinsa, bayan mutuwarsa.
Wani rahoto ya bayyana cewa ’ya’yansa uku, Prince Michael Jr, dan shekara 17 da Paris Michael, ’yar shekara 16 da kuma Bracket Michael II, ‘yar shekara 12 tuni suka fara jin dadin dukiyar tasu, musamman ma sakamakon yadda ’yan uwan Micheal din da iyayensa suka sasanta rigimar da ke tsakaninsu dangane da gadon dukiyar da ya bari. Sai dai an ce duk da yaran suna kashe kudi, amma dai har yanzu ba su kama kafar mahaifinsu ba wajen yin bushasha da dukiya.