’Ya’yan tsohon mataimakin gwamnan Bauchi sun rasu a hatsarin mota
Hatsarin ya auku ne a ranar Asabar a kan hanyar Bauchi zuwa Azare.
’Ya’yan Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, sun rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a hanyar Bauchi zuwa Azare.
Mustapha da Ummi, sun rasu sakamakon hatsarin mota a ranar Asabar, yayin da wasu da ke cikin motar suka jikkata wanda tuni aka kai su asibiti.
- Real Madrid ta ɗauki Denzel Dumfries daga Inter Milan
- Gwamnatin Najeriya ta ɓoye kusan N9trn don tunkarar Zaɓen 2027 — Atiku
An kai gawarwakinsu wani asibiti da ke Bauchi, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
An yi jana’izarsu a Fadar Sarkin Bauchi, inda ɗaruruwan jama’a suka halarta, kafin daga bisani aka binne su bisa koyarwar addinin Musulunci.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana alhininsa kan lamarin.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shi Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce rasuwar babban rashi ne ga iyalan Sanata Baba Tela da kuma ɗaukacin al’ummar jihar.
Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansu da rahama, Ya sanya su Aljannatul Firdausi, Ya kuma bai wa iyayensu haƙurin jure rashinsu.
Haka kuma ya yi fatan Allah Ya tashi kafaɗun waɗanda suka jikkata.