’Ya’yan tsohon shugaban Ghana sun fice daga jam’iyyar NDC
’Ya’yan tsohon Shugaban Ghana Jerry John Rawlings, wanda ya kafa jam’iyar NDC mai mulki, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar mahaifiyarsu wato National Demokratic Paty (NDP)Amina da Yaa Asantewa Rawlings sun zauna a sahun gaba a wurin babban taron wakilai na NDP da akayi a karshen mako a dandalin Trade Fair Site da ke birnin Accra, […]
’Ya’yan tsohon Shugaban Ghana Jerry John Rawlings, wanda ya kafa jam’iyar NDC mai mulki, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar mahaifiyarsu wato National Demokratic Paty (NDP)
Amina da Yaa Asantewa Rawlings sun zauna a sahun gaba a wurin babban taron wakilai na NDP da akayi a karshen mako a dandalin Trade Fair Site da ke birnin Accra, sun bayar da cikaken goyon bayansun ga mahaifiyarsu Nana Konadu Agyeman-Rawlings wacce aka tsayar a matsayin ’yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar.
Har ila yau, an gan su suna bayar da gudunmuwa a shirye-shiryen da akayi tare da mahaifiyarsu.
’Yan matan biyu sun sanya taguwa (T-Shirt), wadda a jikinta aka rubuta “Muna kaunar NDP”, yayin da tsohon shugaban kasar wanda shi ma ya halarci taron don baiwa mai dakinsa goyon baya,inda ya bayyana sanye da suturar Afirka da bakin wando.
Sai dai ita babbar diyar Rawlings, Dokta Zenator, wadda take fatan zama ’yar majalisan a karkashin jam’iyyar NDC ba ta bayyana wurin taron ba.
Kodayake, ta lashe zaben fidda gwani na NDC, amma dan majalisar mai ci, Ishmeal Nii Armah Ashittey da wasu magoya bayan NDC a mazabar sun yi karar ta cewa ba ta cancanci shiga takarar zaben fidda gwanin ba. korafin su shi ne ba ta da rajistan masu jefa kuri’a lokacin da kwamitin tantancewa na jam’iyyar NDC ta ba ta damar shiga takarar, masu korafin suna cewa ta saba wa kundin tsarin jam’iyyar ne da ma na tsarin mulkin kasar na 1992.
Dokta Zenator dai yanzu da yake an sake bude rajistan masu zabe na dan wani lokaci, za ta iya amfani da wannan damar don tabbatar da cewa sunanta ya shiga cikin Biometric Registration na kasar.
A karshen babban taron wakilan jam’iyyar NDP mai dakin Rawlings ce aka zaba babu hammaya ta jagoranci jam’iyyar.
Bayan hukumar zabe ta gabatar da sakamakon Mrs Rawlings ta yi kira ga mambobin jam’iyyar da su mara mata baya ta samu nasara kada Shugaba Mahama.