‘Ya’yan Yau!

Wata hikima ta Ubangiji da yawancin mutane ba su cika kula da ita ba, ita ce yadda muke wanzuwa da rayuwa da girma da hayayyafa ta hanyar ciki da haihuwa. Idan da Ubangiji bai tanadi ciki da haihuwa ba, to da tuni rayuwa ta kare, domin tsofaffi za su yi rayuwa, su wuce, su kuma […]

‘Ya’yan Yau!

Wata hikima ta Ubangiji da yawancin mutane ba su cika kula da ita ba, ita ce yadda muke wanzuwa da rayuwa da girma da hayayyafa ta hanyar ciki da haihuwa. Idan da Ubangiji bai tanadi ciki da haihuwa ba, to da tuni rayuwa ta kare, domin tsofaffi za su yi rayuwa, su wuce, su kuma }anana za su girma, su tsufa, su wuce. Idan da ba a tattali hanyar da idan wasu sun tafi, wasu za su gaje su ba, da tuni an yi karkaf!

To sai dai yawanci ba mu cika nazarin irin wannan baiwar da Allah ya yi wa halittunsa ba. A tsakanin al’ummar duniya, musamman ma dai Hausawa, za ka ga cewa mun fi mayar da hankali ne kan ‘ya’yan da muka haifa, ba tare da dubi ga ‘ya’yan da wasu suka haifa ba. Muna da tunanin cewa dana ko diyata su ne nawa, na wani kuwa, na wanin ne! Wannan shi ke sa a lokutta za ka ga wasu ba su damu da halin da ‘ya’yan wasu ke ciki ba, sai dai nasu. Wannan tunani shi ke lalata tarbiyya da son juna da samar da ingantacciyar zamantakewa.

Ke nan ya dace mu fahimci cewa duk wani da ko diyar da ka ci karo da shi ko ita a bisa doron kasa to ka tabbata da wadda ta duka ta haife su. Kuma da yake mace ba ta haihuwa ita kadai, dole wadannan ’ya’ya suna da mahaifi da ya samar da su a wannan duniyar. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba sai ganin cewa shi Allah Buwayi, Sarkin kowa da komi, da ya shirya da tsara wannan rayuwa, shi ya tsara cewa dole ne a haifa, kyauta ce da ya jefa ta tsakanin halittu, ba tare da sun nema ba.

Ke nan ba wani dalili da mutum zai dauka cewa shi nasa ’ya’ya, su ne ’ya’ya, ’ya’yan wani ko wata ko wasu, ’ya’yan wasu ne kurum.  Babu dalili, domin shi wanda ya haifa bai da wata hujja da zai dogara da ita mai nuna cewa, shi ya zo ke nan duniya, zai kuma rayu da shi da matansa da ’ya’ya, na har abada. Ba wannan ba ma, ko kuma muna zaton ba za mu taba neman taimakon wani daga cikin dangin mutane ba game da kanmu ko namu’ya’yan? Shin muna ganin cewa domin shi Allah ya yi mana zarafi ko ya rufa mana asiri ta yadda ba mu bukatar taimakon wani ko kuma su ’ya’yan namu ba su bukatar taimako daga wani, shi ke nan mu mun fi kowa a doron kasa?

Ko ba komi kamata ya yi mu sani cewa idan mu ne yau, to ba mu ne gobe ba. Idan har wasu za su rayu da nasu ’ya’yan, akwai wa]anda ba za su rayu ba, balle su ga girman nasu ’ya’yan. Haka wasu kuma za su mike tare da ’ya’yan nasu, su haure, su bar su a doron kasa. Kai ba ma wannan ba, nawa ake haifa daga cikin ’ya’ya, uwar ta mutu wajen haihuwa, uban na gudu domin ya kai su asibiti, ya fadi, ya mutu, su tashi ba uwar ba uba?! Wannan ba sai an kirga ba.

Idan haka ne, wanda hakan ne, to, me ya sa ’ya’yan wane sai su kasance ’ya’yan wane kurum, wai don shi ya haife su?  Me ya sa ake ta kokarin nuna wa duniya cewa wancan dan Amina ne, amma ba dan  Halima ba, domin kurum ita (Amina) ce ta durkusa ta haife shi ba (Halima) ba?  Me ya sa?  Amsa wadannan tambayoyi ba zai yi wahala ba, musamman idan mun fahimci cewa kamata ya yi da ya kasance dan kowa. dan nan baki ne ko fari. Daga tsatson mai arziki ko na talaka ya fito. Sai dai kafin mu koma ga wadannan tambayoyi ya dace mu yi tsokaci kan yadda da kan kasance dan duka duniya, ba wai na mahaifansa ba.

Idan haihuwa ce kadai ke sa wasu su zama mutane to da wasu sai dai su karata a doron kasa, ba tare da samun girma da daukaka ba. Akwai yau a doron kasa ‘ya’yan da ba su san iyayensu ba, ba su taba jin labarinsu ba, amma suna cikin hamshakan masu kudi da fada-a-ji a duniya. Wasu daga cikin irin wadannan ‘ya’ya, sun tashi ne kurum suka tsinci kan su a titi, wannan bai hana su girma, su zama wani abu ba!

Akwai wadanda a kullum kuka suke faman yi ganin cewa sun rasa iyayensu, wai ta yaya za su zama wani abu nan gaba! Su ne kullum famar kewar iyayensu, suna fada a cikin zuci cewa da iyayensu na da rai da sun kasance masu farin ciki da jin dadi. Suna ganin cewa suna cikin wannan hali ne domin su ma ba ’ya’yan wane ba ne, to amma za su girma, su kasance iyayen wane, domin su kuma Allah ya kudurta sai sun haifa.

Ke nan wannan ya nuna mana cewa ashe dan da ya tashi cikin daula da mulki da isa ba dole ba ne ya kasance wani abu a doron kasa ba, domin kawai yana tare da iyayensa. Su kuma wa]ancan ‘ya’yan da ba su da uwa da uba, ko kuma suka mike cikin talauci da kunci, suna iya zama wani abu, domin ba iyaye ne ko arziki da mulki da isa ke yin mutum ba, Allah ne!  Me nake son na ce ke nan? ’Ya’ya, duk inda muka gan su, kamata ya yi su kasance ’ya’yan kowa da kowa, domin ba wanda ya san gawar fari, balle kuwa ta karshe. Wannan an da muke ganin cewa ba kowan kowa ba ne, dan, dan uwa ne, dan makiyi ko abokin adawa ne, dan almajiri ne, dan talaka ne, kai kowane iri. Wannan dan daga gidan marayu ya fito, kai ko daga ina yake, idan dai yana shakar iska, dole ya rayu, abin da zai zama kuma ba mu ne masu shatawa ba! Idan muna jin cewa ai wancan dan da ke banga da shaye-shaye da yawon banza da ashararanci, tun da ba danmu ba ne, can ga su Gada, mun yi babban kuskure!  dan da ba namu ba, wata rana zai fiye mana namun! Idan muka yi watsi da shi ko ita, ba ruwan mu da shi ko ita,  mu namu ’ya’yan kawai muka sani, wata rana wannan ]an da muka raina, zai iya gyaruwa, zai iya girma, zai iya zama mutum, zai iya kasancewa shugaban namu dan ko kuma ya shugabance mu, mu kanmu!. Saboda haka hakilon me mutum yake yi dangane da sai dai nasa ’ya’yan su kasance cikin koshin lafiya da walwala; su sami ilmin kwarai ko matsayin kwarai ko kuma su kasance na kwarai a rayuwa, ba sa bukatar ganin haka ga dan wani?  Me wannan tunani zai amfanar gare mu?

Za Mu Ci Gaba